✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Barayi sun kashe mutum 22 a Zamfara

Wasu da ake zargin ‘yan fashi da makami ne sun kashe akalla mutum 22 a kauyen Malikawa da ke lardin Gidan Goga a karamar hukumar…

Wasu da ake zargin ‘yan fashi da makami ne sun kashe akalla mutum 22 a kauyen Malikawa da ke lardin Gidan Goga a karamar hukumar  Maradun ta jihar Zamfara.

Yankin Gidan Goga ya dade yana fama da hare-haren wasu ‘yan bindiga da ke amfani da babura a kwanakin baya.

‘Yan fashi da makami da barayin shanu sun kashe mutum 60 a kauyuku bakwai duk a yankunan lardin daga watan Mayu zuwa Yuli na shekarar 2018.