✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

barawo da Maigida

Wani barawo ne ya shiga gidan wani don yin sata. Ashe mutumin yana kallonsa a lokacin da ya shiga dakin da yake kwance don babu…

Wani barawo ne ya shiga gidan wani don yin sata. Ashe mutumin yana kallonsa a lokacin da ya shiga dakin da yake kwance don babu wuta. Da barawon ya yi yunkurin daukar masa kaya sai maigida ya yi motsi, nan take barawon ya fita a guje. Maigida ya bi shi da gudu da makami. Ashe ba makami ba ne, shantun da matarsa ke wasa ne ya dauka don babu makami a dakin. Maigida na bin barawo, shi kuma barawo ya takarkare don kada ya kama shi. Da suka isa iyaka sai maigida ya ja ya tsaya yana haki, maimakon ya yi shiru sai ya kada baki ya ce: “Allah Ya so ka da ka sha shantu.” Da jin haka sai barawon ya ce: “Dama shantu ne?” Nan fa ya juyo ya bi maigida, shi kuma ya ranta cikin na kare.”
Daga Ahmed Garba Mohammed, 08028797883