✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Barau, Doguwa da Kawu sun halarci jana’izar surukar Ganduje

An yi jana'izarta da misalin ƙarfe 2:30 na rana a gidan Ganduje da ke Kano.

Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau I. Jibrin, Sanata Abdurrahman Kawu Sumaila da wasu sun halarci sallar jana’izar surukar shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje a Jihar Kano.

Limamin Masallacin gidan Ganduje da ke kan titin Miyangu a Kano, Sheikh Auwalu Khalid ne, ya jagoranci jana’izar da misalin ƙarfe 2:30 na rana.

Marigayiyar, Hajiya Asiya Muhammad Gauyama, ta kasance mahaifiya ga mai ɗakin Ganduje, Hafsat Umar Ganduje.

Sarki Aminu Ado Bayero ya samu wakilcin shugaban ma’aikatansa, Alhaji Ahmadu Ado Bayero.

An birne marigayiyar a maƙabartar Tarauni da ke Kano.

Tun da farko, Ganduje ta bakin babban sakataren yaɗa labaransa, Edwin Olofu, ya sanar da rasuwar marigayiyar.

Manyan ’yan siyasa daga jami’yyar APC da wasu jam’iyyun ne suka halarci jana’izar.

Daga cikinsu akwai tsohon manajan daraktan hukumar kula da tashoshin jiragen ruwa ta Najeriya (NPA), Arc Aminu Dabo, tsoffin kwamishinoni da shugabannin ma’aikata.

Sauran sun haɗa da jiga-jigan jam’iyyar APC na ƙasa da na ƙananan hukumomi da sauran ɗaukacin al’ummar Musulmi.