✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Bambancin kayyade iyali da tazarar haihuwa —Dokta Maryam

Hukumar Lafiya A Matakin Farko ta Jihar Gombe ta ce matan jihar sun rungumi tsarin bayar da tazarar haihuwa hannu bibbiyu. Darakta a Hukumar, Dokta…

Hukumar Lafiya A Matakin Farko ta Jihar Gombe ta ce matan jihar sun rungumi tsarin bayar da tazarar haihuwa hannu bibbiyu.

Darakta a Hukumar, Dokta Maryam Abubakar, ta ce matan da suka rungumi tsarin sun bayyana cewa iyalansu na kasancewa cikin koshin lafiya, bayan sun fara bayar da tazarar haihuwa.

“Bayar da tazarar haihuwa ba yana nufin kayyade haihuwa ko hana mace ta haihu ba ne.

“Yana nuna cewa mace za ta samu hutu ne a tsakanin haihuwa da haihuwa, wanda hakan da zai taimaka mata yaranta su yi kwari”.

Ta bayyana haka ne a bayaninta kan bayar da tazarar haihuwa da kayyade iyali, jim kadan bayan taron fadakar da ’yan jarida don fadakar da al’umma kan muhimmancin bayar da tazarar haihuwa.

Dokta Maryam Abubakar ta bayyana cewa mahaifar mace kamar zani ne, idan ana yawan wanke ta babu hutu, ba za ta yi karko ba, shi ya sa ake da bukatar ta samu hutu.

Ta kuma ce bayar da rata a tsakanin haihuwa zai sa yaran kan su su iya taimakon junansu.

A cewarta, akwai kananan cibiyoyin lafiya 497 daga cikin sama da guda 500 da ke fadin jihar suna aiwatar da shirin bayar da tazarar haihuwar.

Sai dai ta ce duk da haka akwai wadanda ba su karbi shirin ba, don haka take kiran su da su rungumi shirin saboda zai taimake su a rayuwa wajen samun iyalai masu nagarta.

Daga nan sai ta ce shirin na bayar da tazarar haihuwar a duk cibiyoyin lafiyar da ke jihar kyauta ne, kuma wasu allura ne ke karbar su wasu kuma kwayar magani ake ba su wasu na mahaifa ake sa musu.

A cewar Dokta Maryam alkaluma sun nuna cewa mata kashi 17 ne cikin 100 ne suka karbi shirin, kamar yadda binciken masana ya nuna.

Sannan ta ce bayan cibiyoyin lafiya a matakin farko da suke bayar da kulawa kan shirin manyan asibitocin jihar suna bayarwa.

A zantawarta Aminiya, Hajiya Lami Abdullahi, wacce ta rungumi shirin bayar da tazarar haihuwa da hannu biyu tace yana taimaka wa mace wajen ta samu karin lafiya wanda zai sa ita da abin da ta haifa su yi karko.

Lami, ta ce, “Duk irin matan da muke gani muke sha’awar ganin su lafiyayyu, ka ga mace tana da ’ya’ya biyar ko bakwai amma za ka dauka ba ta haife su ba saboda lafiya tana ba da tazara ne.

“Duk macen da ba ta ba da tazara idan ta shekara 40, idan ka gan ta za ka dauka ’yar shekara 55 ce ko sittin saboda yadda ta wargaje.”

A gefe kuwa wata da ke ganin bayar da tazara a matsayin kayyade haihuwa, Jummai Samanja, ta ce ita kam ba abin da zai sa ta bada tazara domin “Yawan ’ya’ya ai albarka ne wa ya san mai amfani a ciki, kuma ai ko lokacin zamin Jahiliya ba a kayyade haihuwa.”

Ta ce kara da cewa ita a wajenta babu bambanci tsakanin bayar da tazarar haihuwa da kuma kayyade iyali, shi ya sa ba ta yi kuma ba za ta yi ba.