“In banda dagewar Shugaba Goodluck Jonathan da irin hikimar da ya rika nunawa cikin tafiyar da harkokin jam`iyyar PDP, da tuni jam`iyyar ta ruguje, bisa ga la`akari da irin mugun alkaba`in da wasu shedanun `yan jam`iyyar suka dukufa akai, da aniyar su ruguzata.”
“Na yi iyaka cin iyawata wajen ganin na dora jam`iyyar PDP akan tsarin da yake shi ne, kamar yadda ake siyasa a duniya . Na shigo da tunanin yadda zan gyara tsarin tafiyar da jama`iyyar akan yin zabe ba nadi ba, da kuma tsarin yarjejeniya ba dorawa ba. Ashe! Ba haka ba ne daga wadanda suke ganin wancan tsohon tsari sai ya dore bisa ga son zuciyarsu.”
Wadannan kalamai na sama na daga cikin kalaman da aka ji tsohon shgaban jam`iyyar PDP na kasa baki daya Alhaji Bamanga Tukur yana yi a gidansa da ke Abuja a karshen makon jiya, lokacin da wasu Malaman addini suka kai masa ziyara, kuma sukai yi masa addu`a. Rikici ya yi rikici ne, wanda ya zama matsin lambar da ta tilasta wa Alhaji Bamanga mika wa shugaba Jonathan takardarsa ta sauka daga kan mukaminsa a ranar Alhamis din makon da ya gabata, bayan da ya shafe shekara biyu yana jan ragama (wato daga 24-03-12 zuwa 16-01-14).
Idan har da gaske ne Alhaji Bamanga ya furta wdannan kalamai, akan ya zo da niyyar ya gyara tsarin tafiyar da jam`iyyarsu ta kowane fanni, to, kuwa akwai babban aiki a cikin tafiyar da mulkin dimokuradiyyar kasar nan, bisa la`akari da cewa shi kansa ya san cewa tsarin da ya kawo shi kan karagar mulkin jam`iyyar tun farko, ba irin wancan tsarkakken tsarin da yake begen ya tafiyar da jam`iyyar ba ne, don haka, ya ya zai iya gyara kazanta da kazanta, sannan kuma ya ce zai kai ga nasara?
Mai karatu, in baka manta ba, tun a ranar 21-03-12, da jam`iyyar PDP shiyyar Arewa maso Yamma ta yi babban taronta a Bauchi, da aniyar ta darje wajen zaben `yan takarar da aka raba wa shiyyar don babban zabe na kasa da aka yi a Abuja ranar 24-03-13, ba Alhaji Bamanga Wakilan zaben na shiyyar suka zaba ba, Alhaji Musa Babayo suka zaba, wanda tun daga Bauchin ta tabbata mutanen shiyyar ba su son ya shugabance su balle kuma kasa baki daya. Amma saboda shi Alhaji Bamanga, shi ne dan takarar da shugaba Jonathan ransa ya fi kwantawa da shi, sai ga shi da aka je Abuja, sunansa ya bayyana a jerin `yan takarar 11, inda ana daf da kada kuri`a saura 10 suka janye, suka ce sun bar wa Alhaji Tukur, inda ya ci ba hamayya. Ka ga ke nan tun wancan zabe an fara saka da mugun zare, batun a ce za a samu shugabanci da zai saita alkiblar da take ita ce ta kare.
Bayan Alhaji Bamanga ya hau kan karagar mulki, wani daga cikin matakin da ya fara dauka, a cikin watan Oktoban shekarar 2012, wanda kuma shi ya fara hada shi da gwamnonin jam`iyyarsa, shine, na yin amfani da Kwamitin ayyuka na kasa baki daya na jam`iyyar, wanda ya rushe shugabancin reshen jam`iyyar jiharsa ta Adamawa da ke karkashin jagorancin Alhaji Umaru Ku gama, da ake kallon mai biyayya ne ga Gwamna Murtala Nyako ne, ya sa Kwamitin riko a karkashin jagoracin Jakada Umaru Damagun.
Kodayake a ranar 8 ga watan Janairun bara wasu daga cikin wadancan `yan kwamitin ayyuka na kasa sun tsame kansu daga wancan mataki. Abin da ya kwantar da wancan rikici cikin jam`iyyar PDP a jihar ta Adamawa, shi ne canja shekar da wasu gwamnoni 5, na PDP suka yi a ranar 26-11-13, zuwa jam`iyyar APC, wanda cikinsu har da Gwamna Murtala Nyako, kamar yadda aka samu a sauran jihohin hudu.
A karkashin jagorancin Alhaji Bamanga ne, aka samu kafa kungiyar gwamnonin jam`iyyarsu ta PDP (mai gwamnoni 23, a lokacin da yanzu da suka koma 18) aka danka ragamar shugabancinta ga Gwamnan Jihar Akwa Ibom Godswill Akpbio. Sannan kuma aka samu rigimar sake zaben gwamnan jihar Ribas Cif Rotimi Amaechi karo na biyu a zaman shugaban kungiyar gwamnonin kasar nan da kuri`u 19, amma sai jam`iyyar PDP a karkashin Alhaji Bamanga, ta kekasa kasa ta ce taba amince da zaben ba, don haka gwamnoni 16, magoya bayan shugaba Jonathan, suka yi nasu zaben, inda suka zabi gwamnan jihar Filato, Jonah Jang, a zaman nasu shugaban. Ana cikin irin wannan rudani Alhaji Bamanga Tukur ya dakatar da gwamnonin jihohin Ribas da na Sakkwato, da hanzarin cewa sun yi rashin ladabi ga shugabancin jam`iyya, kodayake daga baya an janye dakatarwar Alhaji Aliyu Magatakarda na Sakkwato. Mai karatu, dukkan wadannan matsaloli da makamantansu, sun zafafa ne bisa ga aniyar da shugabancin Alhji Bamanga yake da shi na tabbatar da cewa a zabubbukan badi, jam`iyyarsu ta PDP da jagoransu, shugaba Jonathan, sun kai bantensu.
Wata babbar rigimar da ake ganin ita ta kara iza wutar Alhaji Bamanga ya bar kujerarsa ba shiri, duk kuwa ya rika cika baki yana cewa ba wanda ya isa ya sauke shi, koda kuwa shugaba Jonathaan, sai dai babban taron jam`iyyarsu, ita ce ta canjin shekar da gwamnonin jam`iyyar biyar daga cikin bakwai suka yi zuwa APC, gwamnonin da suka tsaya, kai da fata akan lallai sai Alhaji Bamanga ya sauka daga kan mukaminsa, da kuma irin yadda `yan kwamitin zartaswa da na ayyuka da kwamitin amintattun jam`iyyar da shugabannin jam`iyyar na jihohi 36 da Abuja, sannu a hankali suka rika janye goyon bayansu akan shugabancinsa, al`amarin da yakai fagen sau biyu yana kiran taro kamar yadda ya saba a gidansa, amma aka yi mai kunnen uwar shegu. Su ma gwamnonin da ake rigimar da su sun karade kasar nan da yawo, inda suka bi duk wanda ya isa, musamman a cikin harkokin kasar nan da tafiyar da jam`iyyarsu, suna nemansu da su sa baki akan yadda shugaba Jonathan da Alhaji Bamanga suke tafiyar da jam`iyyarsu kafin abubuwa su kazanta, amma dai ka ce ba su ci nasara ba, tunda a ranar 26-11-13, gwamnoni biyar daga cikin bakwai suka yi bankwana da jam`iyyar zuwa ta APC, baya ga `yan Majalisun Dokoki na kasa da suka bisu.
Yanzu dai abin tambaya shi ne, tsakanin gwamnonin PDP din nan 5, da Alhaji Bamanga, wa ya ci nasara? Don an ce wai babban burin Alhaji Bamanga na zama shugaban PDP, shi ne yadda zai tabbatar da dan cikinsa ya zama gwamnan jiharsu ta Adamawa a badi in Allah Ya kaimu. Su kuma gwamnonin burinsu, shine daya daga cikinsu ya gaji shugaba Jonathan. Ga Alhaji Bamanga shawarata ita ce ta wakar marigayi Haruna Uji da yake cewa ‘In an girma a san an girma don Allah a rika tunani.”
Bamanga da Gwamnoni: Wa ya yi nasara?
“In banda dagewar Shugaba Goodluck Jonathan da irin hikimar da ya rika nunawa cikin tafiyar da harkokin jam`iyyar PDP, da tuni jam`iyyar ta ruguje, bisa…