Duk wanda ya san Balaraba Ramat Yakubu, to ya san wasu daga cikin rubuce-rubucenta wadanda suka nuna wa mata cewa za su iya sauya rayuwarsu yadda suke so.
Wadansu daga cikin wadannan rubuce-rubuce dai sun yamutsa hazo, lamarin da ya sa aka dauki lokaci mai tsawo ana muhawara a kansu.
- Tauraruwar Arewa: Watan girmama matan Arewa ya tsaya
- Natasha Hadiza Akpoti: Jagorar gwagwarmaya da kasuwanci
Littattafan da Balaraba Ramat Yakubu ta rubuta dai guda tara ne – daya daga cikinsu ma, Wa Zai Auri Jahila, har fassara shi aka yi zuwa harshen Ingilishi.
Bugu da kari, hudu daga cikin wadannan littattafai suna cikin littattafan da ake karantawa a makarantu a Jihar Kano a darussan Adabi.
Sannan kuma wasu daga cikin littatafan Tauraruwar ne jigon bincike ko makaloli da dama da aka wallafa a manyan makarantu a sassan duniya daban-daban.
Kalubalen rayuwa
A hirarrakin da ta yi da kafafen yada labarai daban-daban, Balaraba Ramat Yakubu ta bayyana irin kalubalen da ta fuskanta a rayuwa.
A bisa al’ada, a gidansu ba a saka ’ya’ya mata a makarantar boko – lamarin da ya sa mahaifiyarta ta tura ta makarantar firamare a sirrance.
Lokacin da asiri ya tonu, tana shekara 12 da haihuwa, aka yi mata aure da wani mutum wanda ya ninka ta a shekaru har kusan sau hudu.
Tashin hankalin da ta fuskanta a lokacin da kalubalen da ta fuskanta su ne suka zama jigon Wa Zai Auri Jahila.
Ilimi jari
Amma fa wannan kalubale da ta fuskanta bai sa Balaraba Ramat Yakubu ta karaya ba har ta yi watsi da burinta na yin karatu.
Don haka bayan fitowarta ta ci gaba da karatu har ta kammala karatun firamare ta kuma yi makarantar yaki da jahilci.
Baya ga littatafai kuma, Tauraruwar tamu ta rubuta/tsara labaran finafinai da dama, ta kuma shirya wasu.
Wasu daga cikin finafinanta sun samu lambobin yabo na gida da na waje.
Alal misali Juyin Sarauta ya samu lambobin yabo akalla guda 15, wadanda suka hada da Fim Mafi Kyau a Harshen Najeriya a Bikin Baje Kolin Finafinai na Duniya na Lekki a Legas, 2019, da Fim na Gida Mafi Kyau a Bikin Baje Kolin Finafinai na Gida (KILAF) a Kano, 2018, sanna kuma an ambace shi a rukunin Fim Mafi Tsari a Bikin Baje Kolin Finafinan na Daukacin Afirka, a Nakuru, Kenya, 2018.
Ayyukan al’umma
Abubuwan da Balaraba Ramat Yakubu take sha’awa a rayuwarta sun hada da rubutu, da tafiye-tafiye, da kuma taimaka wa marasa galihu.
Sannan ta taimaka wajen horar da marubuta ta hanyar gabatar da makaloli da lakcoci a tarurrukan kara wa juna sani da tarurrukan bita na marubuta daban-daban.
Tauraruwar tamu mamba ce, ta kuma rike mukamai da dama, a kungiyoyin marubuta da na masu shirya finafinai da dama, musamman ma na mata.
Kadan daga ciki su ne Ma’ajiyar Kudi a Gidauniyar Kannywood, da Kungiyar Marubuta ta Najeriya (ANA) reshen Jihar Kano, da Kungiyar Masu Harkar Finafinai ta Najeriya (MOPPAN).
Sannan ta rike mukamin Mataimakiyar Shugaba a kungiyar marubuta ta Raina Kama, da mukamin Sakatariya a Kungiyar Mata Masu Daukar Nauyin Finafinai.
Bayan harkar rubuce-rubuce da finafinai kuma, Balaraba Ramat Yakubu ta jagoranci Gidauniyar Murtala Muhammad.