Cibiyar rajin tabbatar da daidaito a ayyukan majalisa (CISLAC) ta yi bukaci a yi zuzzurfan bincike kan zargin badakalar da ta dabaibaye Hukumar Raya Yankin Neja Delta (NDDC)
Babban Daraktan CISLAC Auwal Musa Rafsanjani ya ce ko da yake sun yaba da musamman binciken kwamiti Majalisar Wakilai bayan umarnin shugaba Buhari na yin hakan, amma suna da shakku kan yadda binciken zai gudana.
Rafsanjani ya ce abin takaici ne matuka yawan bankade-bankaden da ake yi a hukumar wanda ya kunshi yunkurin tsarewa da kuma zarge-zargen cin rashawa a tsakanin kusan dukkan masu ruwa da tsaki a hukumar.
Ya ce, “Mu na so mu yi kira ga Majalisar Dokoki da ta farka don gudanar da muhimman ayyukanta wadanda suka kunshi sanya idanu, samar da nagartaccen wakilci da yin dokoki, samar da ayyukan raya kasa a mazabunsu da kuma guje wa karbar rashawa.
Daga nan cibiyar ta kuma yi kira ga Fadar Shugaban kasa da sauran hukumomin da ke yaki da rashawa da su kara jajircewa wajen tabbatar da yin komai a fili.
Sun kuma yi kira ga Majalisar Dokoki ta gaggauta cimma matsaya kan zarge-zargen da aka gabatar a zaurukanta da kuma tabbatar ba ta yi kasa a gwiwa ba wajen shigo da bangaren shari’a da sauran hukumomin yaki da cin hanci idan bukatar hakan ta taso.