Kwamitin Majalisar Dattawan Najeriya da ke sa ido kan kudaden gwamnati, ya gayyaci Ministar Kudi, Zainab Ahmed da Akanta –Janar, Ahmed Idris, kan zargin badakalar wasu kuddade da yawansu kai naira biliyan 7.5.
Shugaban Kwamitin, Sanata Mathew Urhoghude, ya ce an kudaden wanda na Hukumar Zayyana da Tsare Ababen Hawa NADDC ne, an debe su ne cikin sirri daga asusun gwamnati na babban bankin Najeriya.
- Wacce ta fi kowa tsawon farata a duniya ta yanke su
- ‘Yadda muka fara shirye-shiryen aikin Hajji da kafar dama’
Sanata Urhoghude, ya ce binciken kwamitin ya gano cewa an kwashi kudaden a rukuni biyu, inda karon farko daga cikin naira biliyan 3.8 aka debi naira biliyan 2.8 a shekarar 2005 sannan aka sake dibar wata naira biliyan daya a shekarar 2006.
Rahoton ya nuna cewa, a rukuni na biyu daga cikin naira biliyan 3.7 da aka yasa a asusun gwamnatin, an soma dibar naira miliyan 725 sannan naira biliyan 1 da kuma naira biliyan 2 a lokuta daban-daban tsakanin watan Maris zuwa Dasumbar 2000.
Sai dai yayin da Kwamitin Majalisar ya tuntubi shugaban Hukumar NADDC, Jelani Aliyu, ya ce ba shi da wata masaniya kan kwasar wannan kudade.