An saki fitaccen mawakin nan, Daniel Oladapo, wanda aka fi sani da D’Banj, bayan tsare shi kan zargin karkatar da kudaden shirin N-Power.
An sake shi bayan shafe sa’o’i 72 a hannun Hukumar Yaki da Ayyukan Zamba (ICPC), bisa zarge-zargen damfara da ke da alaka da shirin N-Power.
- Abdulaziz Abdulaziz Ya Zama Gwarzon Binciken Kwakwaf
- An zabi ‘yar Najeriya cikin ’yan jaridar duniya da za su samu horo na musamman
Shirin N-Power dai Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ne ya kirkiro shi a ranar 8 ga watan Yuni, 2016, domin magance matsalolin rashin aikin yi da karfafawa matasa gwiwa.
Aminiya ta ruwaito yadda fitaccen mawakin ya shiga hannun ICPC, bayan kin amsa goron gayyata da hukumar ta aike masa.
A wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma’a, lauyan D’banj, Pelumi Olajengbesi, ya ce an saki mawakin ne bayan hadin kai da ya bai wa hukumar a binciken da take gudanarwa kan lamarin.
Sai dai bai bayyana ko hukumar ta bayar da belin mawakin ba.
Sanarwar ta kara da cewa, “Bayan shafe sa’o’i 72 a tsare ba bisa ka’ida ba da kuma zargin badakala da ake wa Mista Daniel Oladapo (D’banj), hukumar ICPC ta saki fitaccen mawakin da yammacin ranar Juma’a.
“ICPC ta saki D’banj ne bayan ta kasa gano wani laifi a tattare da shi.
“Dole ne mu bayyana wa ’yan Najeriya gaskiyar lamari cewa D’banj bai aikata laifin da ake zargin sa da shi ba.
“Abin kunya ne a daganta badakalar Naira miliyan 900 da irin wannan fitaccen mutum ba tare da wata shaida ba.”