✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Bad Boys: Shekara 1 bayan marin Chris Rock, Will Smith zai dawo fim

Shekara guda bayan sharara wa fitaccen mai gabatar da shirin barkwanci mari a bainar jama’a, jarumi Will smith zai fito a fim din Bad Boys…

Shekara guda bayan sharara wa fitaccen mai gabatar da shirin barkwanci mari a bainar jama’a, jarumi Will smith zai fito a fim din Bad Boys kashi na hudu.

Hakan na zuwa ne bayan kafofin yada labaran duniya da dama sun yi hasashen ba lallai a ci gaba da damawa da Will Smith ba a masana’antar fina-finan ta Hollywood saboda ya wanka wa mai gabatar da shirin barkwanci Chris Rock mari a bikin bada kyaututtuka na Grammy na 2022.

Wani rahoto na BBC na nuna yiwuwar dawowar farin jinin jarumin fiye da na baya nan ba da jimawa ba, saboda yawan masu yi masa fatan alheri bayan bullar sanarwar.

A wani bidiyo da ya wallafa a shafinsa na Instagram, Smith ya ce za su fito ne tare da jarumi Martin Lawrence kamar yadda suka yi a shirin na baya.

Will Smith ya yi bidiyon ne yana kan hanyarsa ta zuwa gidan Martin Lawrence, har zuwa lokacin da ya isa kofar gidan.

Daga nan ne kuma aka ga sun hau wasa da dariya suna batun dacewar amfani da sunan da suka sanya wa kashi na uku na fim din da na hudun, inda suka ce ba za su bai wa masu kallo kunya ba kamar kodayaushe.

Fim din Bad Boys na uku dai shi ne yafi sauran takwarorinsa yin kasuwa a duniya, inda ya kawo kudin da suka fi na daya da na biyun a hade, duk da wasu na alaknta hakan da hauhawar farashin tikitin sinima da aka samu a wancan lokacin.