✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘bacewar’ kudin Sure-P

Shirin (SURE-P) da gwamnati ta bullo da shi a matsayin wata hukuma ta kawo sauki domin rage radadin karin kudin man fetur da aka yi…

Shirin (SURE-P) da gwamnati ta bullo da shi a matsayin wata hukuma ta kawo sauki domin rage radadin karin kudin man fetur da aka yi a bara, hakika bai tsaya da kafafunsa ba balle ya yi tasiri; kuma abubuwan da suke faruwa a baya-bayan nan game da aikin da aka dora masa yana kawo shakku kan zai iya sauke nauyin da aka dora masa. A makon jiya ne Kwamitin Majalisar Dattawa kan shirin SURE-P ya ce ya gano wani gagarumin almundahana kan hakikannin yadda ake tafiyar da kudin shirin. Kwamitin ya yi zargin cewa Naira biliyan 500 da suka kamata a ce an sanya a asusun kwamitin SURE-P din an rasa inda suka shiga. 

dan kwamiin Kabiru Garba Marafa ya ce, ana sa ran SURE-P ya karbi Naira 32 a kowace litar man feur da aka sayar a cikin gida. Ya ce bayanan Kamfanin Mai na kasa (NNPC) sun nuna cewa daga Janairun 2012 zuwa Satumbar 2013 kimanin lita biliyan 25 aka sayar lamarin da ya nuna ya kamata a ba kwamitin SURE-P Naira biliyan 800 ke nan na wata 21. Sai dai kuma Naira biliyan 300 kacal daga cikin wannan adadi aka ba kwamitin SURE-P din. Har yanzu ba a san inda sauran Naira biliyan 500 suka shiga ba, kuma kin bayyanar da jami’ai biyu da alhakin tara kudin janye tallafin don mika su ga SURE-P, wao Ministar Man Fetur Miss Diezani Alison-Madueke da Babban Manajan Daraktan Kamfanin NNPC, Injinia Andrew Yakubu, a zaman sauraron jama’a na nufin za a dauki lokaci kafin a gano inda suka shiga.
Hanyoyin sarrafa kudi ciki har da bayyana yadda aka kashe kudaden shigar da aka samu daga sayar da danyye ko tataccen mai za ci gaba da zama makare da almundahana sakamakon rashin bin ka’ida. Ana yawan samun babban gibi da ba a bayyana dalilin bacewar wasu makudan kudaden da aka samu daga cinikin man fetur a kamfanin NNPC da kuma abin da NNPC ya shigar a Babban Bankin Najeriya (CBN) da kuma abin da CBN ya ba asusun tarayya, (ko yadda abin yake game da) SURE-P.
Rubutu a takarda dag alibi ana yi ne domin a yi almundahana ya zamo jiki a fanin mai a Najeriya, ya alla a wurin haka ne ko a wurin sayarwa. Ci gaba da kamfanin NNPC yake yin a gaza fadin hakikanin man da ake hakowa a kullum ko aka shigo da shi ko aka tace ko aka sayyar babban gazawa ce dag a alama da gangan ake yi domin a ci gaba tabbatar da cewa harkar mai ta ci gaba da zama kafar sace dukiyar kasar nan.
Duk da cewa wasu ayyuka na SURE-P kamar gyara titin jirgin kasa sun nuna ana samun nasarar, babban makasudinsa ya gaza cimma nasara. Sauran fannonin sun taimaka wajen rashin samun nasarar kirki. Kuma cewa wasu ma’aikatan SURE-P a wasu jihohi a sassan kasar nan suna bin bashin albashinsu na watanni yana nuna rashin gudanuwar shirin a matakan jihohi.
Kasafin yau da kullum wanda ya kunshi makudan kudin da ake kashewa wajen tafiye-tafiyen jami’ai da tallata ayyukan shirin da suke kawo shakku kan alfanun shirin, sun taimaka wajen gaza nasarar shirin.
Ci gaba da cire wani bangare ko daukacin tallafin mai zai dogara ne kan nasarar shirin SURE-P da aka kafa a yanzu. Don haka aiwatar da shi a yanzu bai nuna alfanun janye bangare na tallafin man da aka yi a Janairun 2012 ba. Wannan zai hana duk wani yunkuri na gamsar da jama’a kan alfanun ci gaba da janye tallafin albarkatun man fetur din.
Rusa shirin kamar yadda kwamitin Majalisar Dattawan ya yi barazana ba da shawara a kai, ba shi ne zabin da ya dace ba a yanzu. Kamar kowace hukuma ta gwamnato a kasar nan bin ka’ida sau da kafa da hukunta wadanda suka karya su ne za su kawo gyara tare da tabbatar da nasara.
Kuma gudanar da gagarumin bincike kan zargin bacewar Naira bilian 500 din domin kwato su, abu ne da ya zama tilas, kuma wadanda aka samu da hannu a ciki a tabbatar an hukunta su.