Gwamnatin Jihar Kaduna ta musanta labarin da ke yawo cewa an sace wasu ’yan kasuwa daga Jihar Kano a kan babbar hanyar Kaduna zuwa Abuja.
Kwamishinan Tsaron da Harkokin Cikin Gida na Jihar Kaduna, Samuel Aruwan ne ya bayyana haka a ranar Alhamis.
- ’Yan bindiga sun yi garkuwa ’yan Kasuwar Kantin Kwari 18 a hanyar Aba
- Nuna tsiraici: Bidiyon sabuwar wakar Hausa ya ta da kura a intanet
- Kannywood ta zama kasuwar bukata – Zango
- Dalilin da ya sa na bude gidan abinci- Fati Bararoji
“Gwamnatin Kaduna na bukatar fayyace gaskiyar lamari kan rahoton da ke yawo a kafafen sada zumunta da wasu kafafen jarida cewa masu garkuwa da mutane sun sace adadi mai yawa na ’yan kasuwa daga Jihar Kano a kan babbar hanyar Kaduna zuwa Abuja.
“Har yanzu hukumomin tsaron Gwamnatin Tarayya da ke sintiri a kan hanyar Kaduna zuwa Abuja ba su ba da rahoton wani abu mai kama da wannan,’’ inji Aruwan.
Ya ya ci gaba da cewa, binciken da aka gudanar ya nuna zuwa lokacin da yake bayani babu wani labarin satar mutane da aka yi a Jihar Kaduna.
’Yan bindiga sun yi garkuwa da ’yan kasuwar Kano
Bayanin na Gwamantin Jihar Kaduna na zuwa ne bayan ’yan sa’o’i ’yan mahara sun sace ’yan Kasuwar Kantin Kwari da ke Jihar Kano 18 a kan hanyarsu ta zuwa fatauci a yankin Kudancin Najeriya.
’Yan bindiga sun tare motar ’yan kasuwar ce a Jihar Kogi, suka yi awon gaba da su zuwa cikin jeji, a lokacin da ’yan kasuwan ke hanyarsu ta zuwa garin Aba na Jihar Abiya domin sayen hajoji.
Manajan-Daraktan Hukumar Gudanarwar Kasuwar Kantin Kwari, Alhaji Abba Bello ya tabbatar wa Aminiya cewa, “Suna hayarsu ta zuwa fatauci a garin Aba na Jihar Abiya ne ’yan bindiga suka tare motarsu a kan babbar hanyar Lokoja zuwa Okene a Jihar Kogi.
“Mutane na cewa wadanda aka yi garkuwa da su za su kai mutum 20 ko fiye da hakan, amma adadin da muka iya tabbatarwa shi ne mutum 18,” inji Alhaji Bello.
Aminiya ta tambaye ko ’yan bindigar sun tuntubi iyalan wadanda aka yi garkwar da su ko neman kudin fansa, amma ya ce babu wani bayani game da hakan.
Amma wata majiya ta ce da farko mar garkuwa da mutanen sun bukaci a biya kudin fansa Naira miliyan 50 daga iyalan ’yan kasuwar, kafin daga baya su rage zuwa miliyan 27.
’Yan kasuwar sun bar Kano ne a ranar Lahadi da don zuwa garin Aba a Jihar Abia amma suka gamu da kaddarar.
Kananan ’yan kasuwa da dama a Kasuwar Kantin Kwari kan yi tafiya a motoci zuwa garin Aba, cibiyar kasuwancin Jihar Abiya, domin su sayo yadi ‘Dan Aba.’