Kwalejin Horas da Sojojin Najeriya (NDA) ta musanta rahotannin da ke yawo a kafafen sadarwa da ke cewa an kama wani soja kan zargin hannunsa a harin da aka kai mata watanni biyu da suka gabata.
Mai magana da yawun Kwalejin ta NDA, Bashir Jajira ne ya sanar da haka cikin wata sanarwa da aka raba wa manema labarai a ranar Litinin.
- Jarirai 4 sun rasu a gobarar asibiti a Indiya
- An harbe wani tsohon babban sojan sama da jikansa a Kaduna
Jajira ya ce babu wanda ya kama wannan soja kuma ba shi da wani hadi da wannan hari.
Wasu rahotanni da suka bulla a ranar Litinin sun bayyana cewa an kama Torsabo Solomon, wani jami’in sojan sama mai mukamin Sajan kan zarginsa da taka rawa a harin da aka kai.
Rahotanni sun ce an kama Torsabo bisa umarnin Kwamandan Runduna ta 153 da ke Yola, babban birnin Jihar Adamawa, bayan hukumomin sojojin a Kaduna sun bukaci hakan.
Wasu majiyoyi sun ce sojan dai, wanda ke aiki a wata makarantar sojojin sama da ke Yola, an wuce da shi Kaduna ne a wani jirgin sojoji mai lamba NAF 930 da misalin karfe 8:15 na dare.
Za a tuhume shi ne tare da bukatarsa ya amsa tambayoyi kan bindigu da albarusan da aka yi amfani da su yayin harin.
Aminiya ta ruwaito cewa, a ranar 24 ga watan Agusta ne wasu da ake zargin ’yan bindiga ne suka farmaki kwalejin, inda suka kashe sojoji biyu suka sace wani guda daya, sai dai daga bisani an ceto jami’in da aka sace din.