✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Babu wanda zai bar jami’a don bai biya kudin makaranta ba — Farfesa Sani Tanko

Bana gaba daya Naira miliyan 40 aka ba mu a matsayin kudin gudanarwa.

Shugaban Jami’ar Jihar Kaduna, Farfesa Muhammad Sani Tanko ya kawar da tsoron da iyayen dalibai suke da ita game da kara kudin makaranta inda a tattaunawarsa da manema labarai ya ce babu dalibin da zai bar makaranta saboda bai biya kudin makaranta ba.

Jama’a sun ga sanarwar kun rufe makaranta cewa, masu digiri su zauna a gida har zuwa wani lokaci, me ya kawo haka?

Kamar yadda jama’a suka sani an kara kudin makaranta, wanda hakan ya sa dalibai suka dinga yin zanga-zanga.

Saboda gudun kada a samu matsaloli wadanda duk lokacin da ake zanga- zanga cikin wannan yanayi kada ya zo a kai ga har an rasa rai ne, ya sa muka yanke shawara maimakon mu bar yara su dinga yin zanga-zanga, gara mu kulle makarantar kowa ya zauna hankalinsa ya dawo sannan mu dawo mu zauna mu tattauna.

Shin wannan kulle makarantar ba ku tunanin zai shafi karatun yara musamman la’akari da kwanan nan aka dawo daga hutun annobar Kwarona?

Dalili shi ne in aka bari yara suna zanga-zanga, wadansu
zauna-gari banza suna iya shiga cikin daliban nan su bata abin.

To, kuma ta haka sai an kai ga rasa rai wanda hakan shi ne abin da muke gudu ke nan, kuma ka ga ya fi a kulle makarantar har kowa ya samu natsuwa da ce an samu asarar rayuka da dukiyoyi.

Bayan an samu natsuwa sai mu bude makarantar a zo a ci gaba da karatun cikin natsuwa don idan ba a zaman lafiya, karatu ba zai yiwu ba.

A matsayinku na hukumamakaranta, ba ku yi wani kokari ba ne na ganin kun zauna da yaran nan domin ku fahimtar da su ga dalilin da ya sa hukumar makaranta ta kara kudin makarantar?

Eh, mun zauna da dalibai kamar yadda aka sani, mun zauna da shugabannin dalibai, mun zauna da daliban nan musamman wadanda suke zanga-zangar.

Abin da muke cewa shi ne, akwai hanyoyin da aka yi wadanda za su taimaka. Wanda ba ya da ikon biya, a taimaka masa ya biya.

Mun kawo tsare-tsare wadanda in har dalibai suka bi su in Allah Ya yarda babu wanda zai bar makaranta wai domin ba ya da kudin biyan kudin makaranta.

Abin da muka tabbatar wa dalibai ke nan. Matsalar yanzu ba tasu ba ce. Matsala ce ta iyaye, kuma mu ne iyayen domin haka dukkanmu za mu sa hannu domin ganin an magance wannan matsala.

Da a ce ba a kara kudin makarantar nan ba, abin da kuma ya kamata a koya maka ba a koya maka ba saboda makaranta ba ta da kudin da za ta iya yi maka, gara a kara kudin ya zama an iya ba ka abin da ya kamata, wanda in ka fita za a ce wannan ya samu ilimin da ya dace shi.

A cikin bayaninka ka ce akwai hanyoyin da kuka fito da su domin ganin an tallafa wa wadannan yara saboda su samu su iya biyan wannan kudin makaranta. Wasu irin hanyoyi ne wannan?

Na farko dai akwai tallafin karatu wanda ake kira ‘scholarship.’ Wanda a ‘scholarship’ din ma iri biyu ne; akwai wanda ake ba masu karamin karfi. Akwai na masu kokari da kuma wanda ake ba da bashi wato ‘loan.’

Bayan nan kuma mun tattauna da shugabannin kananan hukumomi sun tabbatar mana za su taimaka wa daliban da suka fito daga kananan hukumominsu saboda su biya kudin makarantar nan.

Sannan bayan haka, mun tattauna da kungiyoyi masu zaman kansu kuma muna fata za su taimaka musamman ma ga wadanda ba za su iya biya ba. Akwai kungiyar mata da suka ce za su taimaka wa mata.

Bayan nan kuma, akwai kungiyoyi na makaranta irin su Majlis da SPSS da sauransu wadanda su ma suka yi alkawarin tallafa wa wadanda suka kasa biyan kudin makaranta.

Saboda haka in dalibai suka yi hakuri, komai zai wuce. Dalibai su yi hakuri kwanan nan za mu bude ‘portal’ inda duk wanda ba zai iya biya ba zai je ya bude ya sanya sunansa.

Ya kamata dalibai su gane, matsalar ba tasu ba ce su kadai. Mu hada hannu mu ga yadda za a yi kowa ya iya biyan kudin makaranta.

Amma idan aka ce a yi ta zanga-zanga, ku ba za ku samu yadda kuke so ba, mu ma ba za mu samu yadda muke so ba. Saboda haka sai ka ga gaba daya an bata goma daya ba ta gyaru ba.

Ka yi maganar wani wuri da za a bude ‘portal’ don duk wanda ba zai iya biyan kudin makaranta ba ya sanya sunansa. Wadanda ba za su iya biya ba ne za su sanya sunansu a ciki?

Duk dalibin da yake ganin ba zai iya biya ba zai sanya sunansa a ciki. Daga baya kuma akwai shugaban dalibai shi zai tantance, eh lallai wane ba zai iya ba. To sai kuma mu ga a ina ne zai iya samun tallafi? Ta kungiyar mata ne ko kuma ta karamar hukuma ce ko kuma ta kungiyar da ke cikin makaranta ce?

Akwai masu tambaya cewa wai dole ne sai an kara kudin makarantar nan. Ko kuma wasu dalilai ne hukumar makarantar take ganin ya kamata a kara kudin makaranta?

Wato yanzu ka ga a bara an ba mu Naira miliyan 420. Bara waccan an ba mu Naira miliyan 580. Amma bana gaba daya Naira miliyan 40 aka ba mu a matsayin kudin gudanarwa wato ‘overhead cost.’ To, Naira miliyan 40 me za ta yi?

Kwamfutocin nan da kake gani dole sai ana saya musu abubuwa. Sannan ko jarrabawar da za a yi sai an sayo takardun jarrabawa.

Ba yadda za a yi a gudanar da jami’a in ba isassun kudi. Naira miliyan 40 da aka ba mu ba ta wuce mu kashe ta a wata daya ba wurin gudanar da jami’ar.

Saboda haka nake cewa idan dalibi an dauke ka an ce za a koya maka a ba ka takardar shaida cewa ka yi digiri a ilimin kwamfuta ko a micro biology, ka je dakin gwaje-gwaje ba kayan da za ka koyi aikin da shi me aka yi?

In kuma kana koyon aikin likitanci ba a je an sayo gawar da za ka zo ka yi aiki a kanta ba, to wane likita za ka zama? Ka ga dole ne jami’a sai da kudi kuma gwamnati ta kasa saboda karancin kudin shiga, ba kudin da za ta bayar wanda zai wadaci jami’a.

Shi kansa wannan kudin makaranta ko an bayar ba wai zai iya daukar nauyin jami’ar ba ce, zai dai taimaka ne kawai.

Abdullah Yunus Abdullah
[email protected]