✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Babu wanda yake da rijiyar mai a Daura – Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce babu mutumin garin Daura guda da yake da rijiyar man fetur a fadin kasar nan. Sabon Shugaban ya bayyana…

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce babu mutumin garin Daura guda da yake da rijiyar man fetur a fadin kasar nan.

Sabon Shugaban ya bayyana hakan ne lokacin da yake ganawa da Aminiya lokacin da manyan Editocin kamfanin suka kai masa ziyara a gidansa da ke garin Daura, ranar Talatar makon jiya. Ya ce: “Kada mutanen Daura suka tsammaci wata alfarma daga gareni saboda ko a lokacin da nake aikin soja basu taba samun hakan ba. Babu mutumin garin Daura guda da yake da rijiyar man fetur a fadin kasar nan. Ina ganin sun amince su rayu akan. Kuma sun kasance mutane masu kirki da fahimta saboda lokacin da na fito daga gidan yari babu wanda ya zo ya nemi wani abu daga gareni. Sun san abin da na mallaka wato gonata da dabbobina da sauransu. Basu ga wani bambanci ba lokacin da nake shugaban mulkin soja,” inji shi.
Dangane da batun janye tallafin albarkatun man fetur ya ce: “daya daga cikin matsalolin da fuskanta bayan ta aikin soja, ita ce aikin da na yi a ma’aikatar man fetur saboda kusan shekara uku da rabi lokacin mulkin gwamnatin sojin Janar Olusegun Obasanjo na yi aiki ne a can a matsayin ministan mai. Gaskiya a duk lokacin da jama’a suke maganar tallafin mai ina shiga cikin rudani. Amma ban ce zan cire tallafi ba ko kuma a’a saboda hakan ya ta’allaka ne da yadda na samu al’amura bayan na kama aiki, kuma na fahimci inda matsalar take. Amma zan yi iya kokarina don ganin na binciko inda matsalar take.”
Da aka tambaye shi dalilin da ya sa ya je Daura gabanin rantsar da shi a yau Juma’a, sai ya ce: “A nan aka haife ni kuma anan ya taso. Ina da ’yan uwana da kuma abokan karatuna. Na yi amannar cewa bayan rantsar da ni akwai dimbin aikin da san a gaba wadanda watakila za su sa na yi makonni ba tare da na waiwayarsu ba. Ina da gona da lambu da kuma dabbobina wadanda zan so na yi masu bankwana.”