✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Babu kudirin kara farashin man fetur a watan Mayu — NNPC

An fara layin mai a wasu yankunan Abuja.

Kamfanin Man Fetur na Najeriya NNPC, ya sanar da cewa babu wani batu na kara farashin litar man fetur a watan Mayu bana.

Manajan Darakta na kamfanin, Mele Kolo Kyari ne ya bayyana hakan ranar Litinin cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta.

Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da Malam Kyari ke ganawa da kungiyar direbobi masu dakon mai (PTD) da kuma ta masu kula da hanyoyi (NARTO).

Kungiyoyin biyu sun samu sabani, lamarin da ya kai ga ta masu dakon man fetur ta yi barazanar shiga yajin aiki.

Sai dai yayin zaman sulhunta tsamin dangartakar da ke tsakanin kungiyoyin biyu da Malam Kyari ya jagoranta, PTD ta sanar da jingine yajin aikin da ta kudiri aniya matukar za’a samu maslaha a tsakaninsu.

“Shugaban kamfanin NNPC yana mai sanar da cewa ba za’a kara farashin man fetur ba a watan Mayu” a cewar sakon da ya wallafa.

Aminiya ta lura cewa ana karancin mai a wasu yankunan Abuja irinsu Katampe, yayin da gidajen mai da dama suka kasance a rufe kuma tuni matasa suka cin kasuwar bunburuntu ta sayar da man fetur a jarkoki.

Sai dai wasu gidajen man sun ce suna tsimayen zuwan hajar ne domin su ci gaba da cin kasuwa.