Shugaban Cibiyar Kwararru kan Aikin Fassara da Tafinta ta Najeriya (NITI), Farfesa Hafizu Miko Yakasai ya kalubalanci amfani da harshen turancin Ingilishi zalla inda ya ce babu kasar da ta taba ci gaba da harshen aro.
Shugaban, wanda kuma malami ne a Jami’ar Bayero da ke Kano (BUK) ya ce kamata ya yi a fara amfani da harsunan gida musamman a bangaren koyarwa saboda ta nan ne amfanin fassara ya shigo.
- Trump ya maka Twitter a kotu kan kin bude shafinsa
- Majalisa na son a fara hukuncin kisa kan barayin kayan jirgin kasa
Farfesan na wadannan kalaman ne yayin wani taro da cibiyar ta shirya a Kano ranar Juma’a domin bikin ranar fassara ta duniya ta shekarar 2021.
A cewarsa, “Shi turancin Ingilishi yare ne kawai kuma bai kamata a rika amfani da shi a matsayin ma’aunin ci gaba ba. Babu kasar da ta taba ci gaba da harshen aro, ta inda fassara ta shigo kenan, akwai alaka tsakanin fassara da ci gaba.
“Yaranmu za su fi fahimtar karatun da ake koya musu idan aka yi amfani da harsunan iyayensu, hakan ne ma ya sa hatta Ministan Ilimi, Malam Adamu Adamu ya ba da shawarar fassara darusan Lissafi da Kimiyya zuwa harsunanmu na gida,” inji Farfesa Hafizu.
Shehin malamin ya ce taken ranar na bana, “Samun daidaito wajen fassara” ya zo a daidai lokacin da aka fi bukata saboda neman daidaita fassara, musamman a kafafen yada labarai a kasar nan.
Farfesan ya kuma bayyana cewa yanzu haka kudurin da ke neman a kyale kwararru kawai su rika yin aikin fassara a Najeriya ya tsallake karatu na daya da na biyu a zauren Majalisar Wakilai ta tarayya.
Tun farko da yake nasa jawabin, Shugaban Sashen Kimiyyar Harshe da Harsunan Ketare na jami’ar, Dokta Isah Yusuf Chamo ya ce shirin na yunkurin daidaita fassarar ya zo a daidai lokacin da ake samun yawan kura-kurai a wajen fassara labarai musamman a kafafen yada labarai a Jihar Kano.
A cewarsa, jami’ar ta jima tana bayar da takardun babban digiri a bangaren na fassara.
A yayin taron dai, an gudanar da rubutacciyar jarrabawa da ta baki ga sabbin dalibai masu son zama mambobin cibiyar ta NITI, a matsayin sharadin zama cikakkun mabobinta.
Hukumar Kula da Ilimi, Kimiyya da Al’adu ta Majalisar Dinkin Duniya (UNESCO) ce dai ta ware ranar 30 ga watan Satumban kowacce shekara matsayin ranar fassarar ta duniya domin nuna muhimmancinta.