Wani malami a cibiyar bincike da koyar da dabarun noma ta Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya Farfesa Salihu Adamu Dadari, ya bayyana cewa babu wani ci gaba da Najeriya ta samu, a fannin aikin noma a shekara 60 da samun ’yancin kai.
Farfesan ya bayyana haka ne a lokacin da yake zanta wa da wakilin Aminiya a Jos.
Ya ce ya kamata a ce a shekara 60 da Najeriya ta yi da samun yancin kanta ya kasance tana noma abincin da za ta iya ciyar da ’yan kasarta, kuma tana fitar da rarar abincin da aka noma zuwa kasashen waje.
Ya ce misali kamar kasar China tana da kashi daya bisa uku na al’ummar duniya; amma bata taba sayen abinci daga waje ba.
“Amma a Najeriya kusan komai na abinci ana shigo mana da shi ne daga waje.”
Ya ce a lokacin da aka sami yancin kan a shekarar 1960 zuwa shekara ta 1985, masakun kasar nan suna aiki.
Manoman auduga suna noma audugar da masaku suke bukata, kuma ana saya har ta yi rara a kai ta kasashen waje.
Ya ce ada Najeriya ce ta daya a wajen noman koko, a kasashe masu tasowa.
Kuma tana noman gyada da kwakwar manja da ake kai wa kasashen waje.
“Marigayi Firaminista Arewa Sir Ahmadu Bello ne, ya bai wa kasar Malesiya irin kwakwar manja da aka dauka daga tsangayar koyar da aikin noma ta Kabba da ke Jihar Kogi, a ka kai musu.
Yanzu kasar Malesiya ita ce ta daya wajen sarrafa manja a duniya.a on haka a ganina Najeriya, ba ta sami wani ci gaba ba a cikin shekara 60 da samun yancin kai ta fuskar noma,” inji shi.
Farfesa Dadari ya yi bayanin cewa a da ba mu da yawa a Najeriya, amma masu yin noman suna da yawa domin a baya kusan kowa yana noma.
Ya ce “A yanzu mun ninka yawanmu amma wadanda suke noman basu kai yawan na da ba kowa ya sa karya a gaba. Matasanmu da dama basu son yin noma.”
Ya ce a fannin tsarin noman an sami dabaru da na sinadirai daban daban na noma amma babu masu noman.
“Babu shakka wannan gwamnati ta yi kokari da ta ce a koma aikin noma.
Domin idan aka sami wadataccen abinci za a sami zaman lafiya da kwanciyar hankali a Najeriya.”
Ya yi kira ga al’ummar Najeriya kan su kama noma tsakani da Allah: “Gwamnati ta tsara hanyoyin da za a rika fitar da abincin da aka noma daga Najeriya zuwa waje.”
Ya ce idan ana fitar da kayan abinci daga Najeriya zuwa waje, hankalin ’yan Najeriya zai dawo jikinsu.