Dan takarar shugaban kasa na Jam’iyyar APC, Bola Tinubu, ya karyata labaran da ke yawo cewa ya yi ganawar sirri a London da gwamnonin PDP biyar masu korafi, da aka fi sani da G-5.
Tinubu ta bakin kakakinsa, Tunde Rahman ya ce, sabanin abin da kafaren yada labarai ke bazawa, babu abin da ya hada shi a London da gwamnonin na G-5, wadanda Gwamnan Jihar Ribas, Nyesom Wike, yake jagoranta.
- Dan uwan dan sanda ya kashe shi ya tsere da bindigarsa
- Muhimman abubuwan da suka faru a duniyar adabi a 2022
Kakakin nasa, ya ce, wadanda suka kitsa rahoton kanzon kuregen tare da iyayen gidansu sun yi hakan ne domin cim ma burinsu na siyasa.
Sanarwar ta ce, “Lokacin da Tinubu yake kasar Birtaniya ya lura da wasu labarai da manyan jaridun Najeriya suka yi cewa ya yi ganawar sirri a Lonon da Gwamnonin G-5 daga Jam’iyyar PDP.
“Ya jajirje kan yakin neman zabe domin samun nasara a zabe shugaban kasa mai zuwa a inuwar Jam’iyyar APC domin aiwatatr da manufar kungiyar da sabunta burinsa ga al’ummarmu a duk bangarorin rayuwa.”