✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Babbar Sallah: An gargadi matasa kan bangar siyasa a Masallatan Idi

Matasa su guji gudanar da duk wasu harkokin siyasa a Masallatan Idi.

Kwamishinan ’yan sandan Jihar Gombe Ishola Babatunde Baba’ita, ya ja hankalin matasa ’yan siyasa da su guji gudanar da duk wata harkar siyasa a masallaci a lokacin gudanar da sallar Idi.

Cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun jami’in hulda al’umma na rundunar ’yan sandan jihar, ASP Mahid Mu’azu Abubakar, Kwamishinan ya ce a shirye suke su kare rayuka da dukiyoyin al’umma a lokacin bukukuwan Babbar Sallah.

Sanarwar ta kuma gargadi matasan akan saba wa dokokin Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) wajen gudanar da ayyukan siyasa gabanin lokacin da shar’anta yin hakan ya cika.

Babatunde ya bayyana damuwa kan yadda matasa ke hana mutane inganta sallarsu cikin nutsuwa ta hanyar daga hotunan ’yan siyasa a lokacin da ake sallah a masallantan Idi.

Kwamishinan ya ce hukumomin tsaro a tsaye suke kyam wajen dakile duk wasu ayyukan batagari da kuma na ’yan ta’adda da suke son tayar da zaune tsaye a fadin jihar.

Kazalika, Kwamishinan ya kira yi iyaye a kan su kula da zirga-zargan ’ya’yansu a lokacin bukukuwan saboda gudun fadawar su hannun batagari.

Ya kuma umurci al’ummar Gombe da kewaye da su rika mika rahoton duk wani motsi da basu yarda da shi ba ga ofishin hukuma mafi kusa don daukar mataki.