Shugabannin jam’iyyar PDP sun ce babban zaben da jam’iyyar za ta yi na fidda gwani zai nuna irin sa’ar da jam’iyyar take da shi a zaben shekarar 2019 tare da nuna yadda masu zabe za su dauki jam’iyyar.
Tsohon Ministan Ilimi kuma Tsohon Jakadan Najeriya a Kasar Jamus, Farfesa Tunde Adeniran da Tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Ibrahim Mantu sun ce taron da jam’iyyar za ta yi a ranar tara ga watan Satumba zai nuna makomar jam’iyya a babban zaben da za a yi a kasar a shekarar 2019.
Da yake bayyana wa duniya sha’awarsa na neman takarar shugaban jam’iyyar a taron da jam’iyyar ta gudanar a Abuja, Farfesa Adeniran ya ce zaben gaskiya ne kawai zai bayar da tabbacin dorewar jam’iyyar a shekaru masu zuwa.