Tunde Mark, babban da ga tsohon Shugaban Majalisar Dattijan Najeriya, David Mark ya rasu ranar Juma’a bayan fama da cutar sankara.
Tuni dai masu fada a ji a Najeriya suka fara mika ta’aziyarsu ga mahaifin margayin, Sanata David Mark.
- Gwamnati ta daukaka kara kan sallamar Kanu da kotu ta yi
- Magidanci ya birkice wa banki kan bacewar N1.5m daga asusunsa
Cikin wata sanarwa da dan takarar shugaban kasa na jam’iyar PDP Atiku Abubakar, ya fitar, ya ce, “Na kadu da mutuwarsa, domin ni da Tunde muna da kyakykyawar alakar da ta sa na dauke shi a matsayi dan cikina.
“Addu’ata ce ga mahaifinsa shi ne Allah, ya ba shi hakurin jure rashin, shi kuma margayin, Ya ji kan sa, Ya sa mutuwar ta zamo hutu gare shi,” in Atiku, ta sanarwar da kakakinsa ya fitar a Abuja.