Mai neman takarar Shugaban Kasa karkashin jam’iyyar APC, Sanata Bola Ahmed Tinubu ya ce ba zai daina siyasa ba har sai ya cika burinsa na son zama Shugaban Kasar Najeriya.
Dan siyasar ya yi wannan furuci ne a Makurdi babban birnin Jihar Binuwai, yayin ziyarar da ya kai Jihar a ranar Talata don neman goyon bayan daliget, gabanin zaben fid da gwani mai zuwa na APC.
- 2023: Tinubu nake so ya gaji Buhari – El-Rufa’i
- Mutum 20 sun mutu a hatsarin mota a hanyar Kaduna zuwa Abuja
Tinubu ya yi kira ga matasan Jihar da su tabbatar sun mallaki katin zabensu, tare da ba su tabbacin shi da mutanesa suna tare da matasan don hada hannu wajen bunkasa hadin kai da ci gaban Najeriya.
“Duk da dai shekarunmu sun ja, za mu bar siyasa nan kusa idan kun so, amma ba zan daina siyasa ba sai bayan na zama Shugaban Najeriya,” inji shi.
Ya kara da cewa, muddin aka zabe shi a matsayin Shugaban Kasa, gwamnatinsa za ta maido wa talakawan Najeriya karsashin da suka rasa.
Kazalika ya ce, idan APC ta tsayar da shi a matsayin dan takararta, babu wata ja-in-ja da za a samu tsakaninsu da dan takarar jam’iyyar hamayya ta PDP.
Daga nan, ya jaddada cewa idan ya samu mulkin kasa zai dora Najeriya a kan salon mulkin da ya yi amfani da shi sa’ilin da yake Gwamnan Legas don samun daidaito.