✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ba zan taɓa goyon bayan wata doka da za ta cutar da Arewa ba — Kofa

Ɗan Majalisar Tarayya mai wakiltar ƙananan hukumomin Ƙiru da Bebeji na Jihar Kano, Abdulmumin Jibrin Kofa ya bayyana cewa ba zai taɓa goyon bayan duk…

Ɗan Majalisar Tarayya mai wakiltar ƙananan hukumomin Ƙiru da Bebeji na Jihar Kano, Abdulmumin Jibrin Kofa ya bayyana cewa ba zai taɓa goyon bayan duk wani ƙudiri ko wata doka da za ta cutar da Arewa ba.

Kofa ya yi bayanin hakan ne a cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Facebook a yammacin ranar Laraba.

A cikin saƙon wanda ya ke iƙirarin an yi masa gurguwar fahimta tare da ba da haƙuri, Kofa ya ce ba ɗari bisa ɗari yake goyon bayan ƙudurorin gyara haraji ba.

“A matsayi na na mai hawa huɗu a Majalisa, ban taɓa ba, kuma ba zan taɓa goyon bayan duk wata doka ko ƙudirin da zai kawo illa ga mazaɓa ta, jihata ko Arewa da ma Najeriya ba.”

A cewarsa, “babu wurin da ko sau ɗaya na ce ina goyon bayan sababbin dokokin haraji ɗari bisa ɗari.”

“Abin da na ce (shi ne) akwai batutuwa da dama waɗanda za su zama alheri ga yankin Arewa da ma Najeriya. Kuma mu ’yan majalisa na yankin Arewa mu yi amfani da rinjayen da muke da shi a majalisa mu yi tsayin-daka mu goyi bayan duk wasu ƙudurorin da za su amfani Arewa ta fannonin bunƙasa tattalin arzikin yankinmu da suke cikin ƙudirorin.

“Sannan mu kuma cire waɗanda za su cutar da mu, ko mu gyara su ta yadda ba za su cutar da mu ba.

“A yayin haka kuma, mu tabbatar da yi wa sauran jihohi da yankunan Nigeria adalci a tsarin dokar. Amma ra’ayin wasu shi ne a yi watsi da dokar gaba ɗaya.”

A cikin saƙon, Kofa ya ƙara da cewa yana so ne yankin Arewa su yi amfani damar dokar wajen bijiro da wasu sabbin hanyoyi, “mu shigar da su a cikin kundin ƙudirorin,” in ji shi.

“Amma duk da haka ina bai wa duk waɗanda matsayata a kan dokar ya ɓata musu rai.

“Ina kuma ba da tabbacin cewa zan yi duk abin da zan yi iya yi, iya ƙarfin ɗan Adam in ga cewa ba a cutar da Arewa ba da kuma ganin an yi wa kowa adalci a Najeriya da kowane lokaci kamar yadda na saba yi.”