✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ba zan lamunci rashawa ba – Kwamishina

Sabon Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Gombe, Muhammad Garba Mukaddas wanda ya karbi aiki a ranan Litinin da ta gabata daga tsohon Kwamishinan da aka yi…

Sabon Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Gombe, Muhammad Garba Mukaddas wanda ya karbi aiki a ranan Litinin da ta gabata daga tsohon Kwamishinan da aka yi wa canji zuwa Jihar Legas, Mista Shina Taitu Olukolu, ya ce ba zai lamunci rashawa da cin hanci daga ’yan sanda ba, kuma jama’a su sani har yanzu beli a wajensu kyauta ne kada kowa ya biya kudi.

Kwamishinan ya bayyana haka ne lokacin da yake ganawa da manyan jami’an ’yan sandan jihar, inda ya ce ya samu labarin suna da kwazo daga wajen wanda ya canja kuma duk wanda ya shirya zai yi aiki da shi a shirye yake su yi aiki tare.

“Bana barci komai dare idona biyu ne, kuma ina zaga ko’ina don ganin yadda aiki ke tafiya da dare,” inji sabon Kwamishinan ’Yan sandan.

Ya shaida wa ’yan sandan cewa zai zaga jihar don gane wa idonsa duk caji ofis din da maharan Boko Haram suka lalata a baya don ganin barnar da ta auku da karbar cikakkun bayanai.

Ya ce ba yana nuna zai ci mutuncin ’yan sanda ba ne, so yake ya farkar da su daga barci, kuma maganar cin hanci a tsaye yake a kan kafafunsa domin ba zai saurara wa haka ba.

Kwamishina Mukaddas, ya kara da cewa bai ce a karbi kwabon kowa ba a kan maganar beli, domin kyauta ne kuma yana nan a kan kyautar.

Da yake jawabi kafin mika ragamar aiki, tsohon Kwamishina Mista Shina Tairu Olukolu, ya ce ’yan sandan suna da kokari don sun ba shi hadin kai kuma ya tabbata shi ma sabon zai samu hadin kai daga gare su.