Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi, da Gwamna Nyesom Wike na Jihar Ribas, sun sake cacar bakin kan siyasa.
Tun 2014 mutanen biyu ke cacar baki har sun taba dambacewa a wani caji ofis a Fatakwal, babban birnin jihar.
- Kansila ya nada mataimaka 18 a Kano
- Ba za mu yi sulhu da ’yan bindiga ba —Monguno
- Na koya wa Ameachi darasi a siyasa —Wike
- An rufe makarantun sakandaren gwamnati a Neja
Bayan bangarorin biyu sun tsagaita da caccakar juna, a ‘yan kwanakin nan, Wike ya yi wa Amaechi shagube da cewa akwai siyasa a ayyukan raya kasa da ma’aikatar ministan ke yi.
Ya ce gwamnati mai ci tana bunkasa layin dogo a yankin Kudu maso Gabas inda Ministan ya fito ne saboda babban zaben 2023.
Amma a wata gugar zana da ministan ya yi wanda ake ganin raddi ne ga gwamnan, Amaechi ya ce shi baya shan giya kafin ya yi magana.
Bayan kalaman nasa ne Wike ya mayar da martani tare zargi Gwamnatin Tarayya da kare Amaechi daga gurfanar da shi kan rashawa.
Ya zargi Amaechi da sayar da kadarar Gwamnatin Jihar Ribas kan Dala miliyan 308 a lokacin da yake gwamna amma Dala miliyan 208 kadai ya sa a asusun jihar.
Ya kuma yi gugar zana da cewa ya koya wa ministan wanda ke ganin kansa fiye da kowa darasi a siyasa.
A hirar da aka yi da shi a wani shirin talabijin na ARISE ranar Alhamis, an nemi Amaechi ya amsa zargin Wike amma ya ce: “Ba ni da lokacin batawa kan maganar gwamnan, na riga na yi magana kuma na yi gaba.
“Shi ma’aikacina ne, ba zan iya kaskantar da kaina ba. Sau biyu ina yin gwamna, na yi Shugaban Majalisa sau biyu, na yi shugabanci na zango na biyu a Kungiyar Gwamnoni, yanzu kuma ni minista ne.
“Ya za a yi in tsaya bata lokacina ina magana a kan shi?”
Amaechi ya mulki Ribas tsakanin 2007 da 2015 kuma Wike na daga cikin mukarrabansa.
A lokacin da yake gwamna Wike ne Shugaban Ma’aikatansa kafin a nada Wiken Ministan a Ma’aikatar Ilimi.
Daga baya ne suka samu sabani a yayin da ak shYa samu sabani ne tare da Amaechi a zaben 2015.