✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ba zan amince da zama a benci a Chelsea ba – Mikel Obi

dan kwallon Najeriya da ke buga wa kungiyar kwallon kafa ta Chelsea da ke Ingila, Mikel Obi ya ce a shirye yake ya bar kungiyar…

dan kwallon Najeriya da ke buga wa kungiyar kwallon kafa ta Chelsea da ke Ingila, Mikel Obi ya ce a shirye yake ya bar kungiyar ta Chelsea idan dai har zai ci gaba da zama a benci.
dan wasan tsakiyar, wanda ya fara buga wa kungiyar Chelsea kwallo tun a shekarar 2006 ya ce duk da yana da sauran shekara daya na kwantiraginsa a kungiyar, idan dai za a bar shi ya ci gaba da zama a benci ne, to lallai zai iya barin kungiyar duk da yana matukar son ci gaba da buga wa kungiyar wasa.
“Ina son in buga wasa ne, ba na son zama a benci ko kadan, kamar yadda na zauna a baya. Don haka in ya kama in tafi, zan tafi domin in samu damar buga wasanni,” inji shi.
kungiyar Chelsea ta zabo Antonio Conte dan kasar Italiya da yanzu haka yake horar da ’yan wasan kwallon kasar Italiya a gasan cin Kofin Nahiyar Turai da ke gudana a kasar Faransa domin ya maye gurbin Guus Hiddink wanda ya bar kungiyar bayan ya yi horarwa na wucin-gadi. Duk da cewa bai riga ya zo ba, amma yana da ikon bayar da sunayen wadanda za a sayo ko a sayar daga kungiyar ta Chelsea. Don haka ne ma Mikel ya ce, sai sabon mai horarwar ya zo, daga nan sai ya ga yadda zai yi.