✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ba za mu daina bincike ba har sai mun gano Janar Alkali – Rundunar Soji

Rundunar Sojin Najeriya ta ce ba za ta daina bincike ba har sai ta gano Manjo Janar (mai ritaya) Muhammad Idris Alkali, wanda aka daina…

Rundunar Sojin Najeriya ta ce ba za ta daina bincike ba har sai ta gano Manjo Janar (mai ritaya) Muhammad Idris Alkali, wanda aka daina jin duriyarsa tun 3 ga watan Satumban bana.

Rundunar Sojin ta bayyana haka ne ta bakin Kwamandan Rundunar ta Uku da ke Jos, Manjo Janar Benson Akinruluyo lokacin da yake amsa tambayoyin ’yan jarida a Jos a ranar Talatar da ta gabata bayan rundunarsa ta sake ciro wata farar bas mai cin mutum18 daga cikin kududdufin da ta ciro motar Manjo Janar Alkali a makon jiya.

Idan ba a manta ba a ranar 20 ga Satumba, rundunar sojin ta fara neman Manjo Janar Alkali a lokacin da ta samu rahoton bacewarsa.

A makon jiya rundunar ta ciro bakar mota kirar Toyota Corolla mai dauke da lamba MUN 670 AA, wadda ita ce motar da Janar Alkali yake tukawa a ranar da ya bace.

Rundunar sojin ta yi nasarar ciro motar ce a ranar Talatar makon jiya a wani kududdufi da ke kauyen Lafendeg a Gundumar Dura Du a Karamar Hukumar Jos ta Kudu, karamar hukumar da tsohon Gwamnan Jihar, Jonah Dabid Jang ya fito.

A cikin motar an samu bakin takalmi sau-ciki na sojoji da gajeren wando da kuma riga T-Shirt mai dauke da sunan M.I Alkali.

Shugaban Rundunar Sojin Najeriya, Laftana Janar Tukur Buratai ne ya kafa bataliyar janye ruwan kududdufin, sannan ya dora alhakin gudanar aikin janye ruwan a wuyan Runduna ta Uku da kuma Rundunar Samar da Zaman Lafiya a Jihar Filato (OPSH).

Idan ba a manta ba, Manjo Janar Alkali ya yi ritaya ne a matsayin Babban Jami’in Gudanarwa na Sojin Najefriya, kuma ya bace ne a lokacin da yake kan hanyarsa ta zuwa Bauchi daga Abuja.

Daga farko rundunar ta samo farin marufin wata bas ce, kafin ta samo motar Manjo Janar Alkali a mako jiya, inda a ranar Talatar da ta gabata kuma rundunar ta sake samun nasarar ciro farar mota bas mai cin mutum 18, mai dauke da lamba Filato, RYM 307 DA.

A lokacin da Kwamandan  Rundunar OPSH, Manjo Janar Augustine Agundu yake tattaunawa da ’yan jarida a bakin kududdufin bayan an ciro bas din, ya ce akwai abubuwan ban mamaki a cikin kududdufin.

Ya ce, “Bayan wannan mota kirar bas mai daukar mutum 18 da muka ciro a yau, yanzu haka muna iya ganin motoci uku a cikin kududdufin, wanda nan ba dadewa za mu rika ciro su daya bayan daya.”

Ya kara da cewa za a ci gaba da ciro abubuwa a cikin kududdufin domin an dade ana jefa abubuwa a cikinsa.

Shi ma a lokacin da yake karin bayani, Kwamandan Runduna ta Uku, Manjo Janar Benson Akinruluyo ya bukaci al’ummar Gundumar Dura Du su ba rundunarsu hadin kai don ta ci gaba da bincike don gano Manjo Janar Alkali.

Ya ce, “Bai kamata su ji tsoro ba, a yanzu mun gano motarsa, abin da ya rage shi ne mu gano shi ko kuma gawarsa, domin an ba mu umarnin mu gano shi ko a mace ko a raye. Idan son samu ne shi ne kada al’ummar Dura Du su wahalar da mu, su fada mana inda suka boye shi, ko suka boye gawarsa.”

Ya kara da cewa rundunarsa za ta ci gaba da janye ruwan har sai sun tabbatar da ko Manjo Janar Alkali yana cikin kududdufin ko akasin haka.

Rundunar Soji ta Uku ta bakin Mataimakin Babban Daraktan Watsa Labarai, Kanar Kayode Ogunsanya ta bayyana cewa jami’ansu sun sake ciro wata jar mota kirar Toyota Saloon a cikin          kududdufin.

Kanar Ogunsanya ya bayyana haka ne ta hanyar aiko da sako ta kafar sadarwar WhatsApp. Ya ce jar motar tana dauke da lamba kamar haka Bauchi, AG 645 TRR.