✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ba riba

Wata rana wani barawo ya sato kaya sai ya ba matarsa ta kai kasuwa ta sayar. Da ta je kasuwa sai aka sace kayan, ta…

Wata rana wani barawo ya sato kaya sai ya ba matarsa ta kai kasuwa ta sayar. Da ta je kasuwa sai aka sace kayan, ta dawo gida ta samu mijinta a cikin jama’a suna hira. Ya ce mata: “An sayar da kayan?” Sai ta ce: “An sayar kamar yadda ka sayo.” Sai ya ce: “Babu riba ke nan.”