✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ba ni na kashe zomon ba: Sharhin littafin dakika Talatin

Sunan littafi: Dakika TalatinMarubuci: Ado Ahmad Gidan DabinoShekarar Wallafa: 2015Kamfanin Wallafa: Gidan Dabino Publishers, KanoFarashi: Ba a fada ba Game da littafin: Littafin Dakika Talatin,…

Sunan littafi: Dakika TalatinMarubuci: Ado Ahmad Gidan DabinoShekarar Wallafa: 2015Kamfanin Wallafa: Gidan Dabino Publishers, KanoFarashi: Ba a fada ba

Game da littafin:

Littafin Dakika Talatin, wani sabon littafin wasan kwaikwayo ne da ya bayyana a rubu’in karshe na wannan shekara ta 2015, wanda shahararren marubuci; Malam Ado Ahmad Gidan Dabino (MON) ya wallafa, a kokarinsa na ganin an samu cike gibin da ke akwai na karancin littattafan wasan kwaikwayo na Hausa, cikin tsari da salo masu armashi, tare da kyautata daba’i.
Samun damar karanta wannan littafi da na yi ya tuna min abubuwa masu yawa. Jin dadin karanta shi da na yi, da la’akari da dumbin darussan rayuwa da aka kunsa cikin littafin, ya zaburar da ni ga kokarin rubuta wani dan sharhi ko nazari kansa, don kara fito da dunkulallun abubuwan da ke cikinsa, duk da kasancewar kamata ya yi wani daga malamaina ne ya fi cancanta da wannan aiki.
Tsari:
Marubucin ya shirya wannan wasan kwaikwayo cikin sassa ko kashi takwas, kamar yadda ya kira tsarin; ya kuma gabatar da shi a farkon littafin kamar haka: 1-Wasu samari a gindin bishiya. 2-Yassar ya shiga neman aure. 3-Shirye-shiryen biki sun kamala. 4-Zannira ta kafa kungiya. 5-An daura aure, ango ya rasu. 6-Bayan kwana Arba’in. 7-Zannira ta shigar da kara. 8-Zannira ta haihu kuma kungiyarta ta shahara.
A karkashin kowanne daga wadannan sassa takwas, akwai fitowa kama daga daya, uku, har ma da kashin da ke da fitowa 19, wadanda aka warware matashiyar kashin cikinsu.
Jigo da warwararsa:
Jigon wannan wasan kwaikwayo shi ne Nusarwa da Fadakarwa, kasancewar an yi kokarin bayyana wata mas’ala ce mai rikitarwa da kan iya faruwa, wadda mutane da dama na iya yin inkarinta, tare da fadakar da masu larurar nakasa kowace iri ce ga muhimmancin dogaro da kai, maimakon zaman Allah-Ya-ba-ku-mu-samu.
Tun farko, an bayyana yadda wasu daga abokan Yassar tare da wata budurwarsa suka cika da mamakin zabinsa na ya auri nakasasshiya (gurguwa). Dubi abin da abokinsa Habu ya ce da shi: “Wai kai me yake damun ka ne, a ce duk yawan ’yan matan da ake da su, amma ka rasa wadda za ka ce kana so sai gurguwa? Ko ka rasa wadda take son ka ne?” (shafi na 1).
Haka ma budurwarsa Samira ta cika da mamaki har take cewa: “Amma don Allah in tambaye ka mana. Shin gurguwar nan ta fi ni ne? (shafi na 4).
Amma duk irin wannan kalubale da Yassar ya fuskanta bai girgiza ba ko kadan. Sai ma cewa ya yi: “Bari na tambaye ka, shin gurguwa ba mutum ce ba? Kuma ai ita soyayya babu ruwanta da gurgu ko mai kafa, haka makaho ko mai ido. In dai maganadisun ya ratsa cikin jini, shi ke nan kawai sai tafiya, mahaukaci ya hau kura.” (shafi na 1).
Duk da wannan tsayuwar daka ta Yassar, shi da masoyiyar tasa sai da suka fuskanci mummunar turjiya daga budurwarsa da ita ta so ya aura, don kuwa sai da ta tari gurguwar da zai aura a hanya, ta kade ta da mota ta gudu. Har ma kawarta na kara zuga ta da cewa: “Amma fa kin birge ni. In ce ko ta yi raunuka?” (shafi na 12).
Wata kawarsu ta so nusar da ita kan wannan danyen aiki da ta yi, amma sai ta ce: “Don Allah rabu da ita. In da za ta mutu ma ai haka na fi so, kin ga sai in samu ranata yadda nake so in yi shanya.” (shafi na 12).
Bayan Zannira ta murmure daga raunukan da ta samu sakamakon kade ta da mota da abokiyar kishinta ta yi, sai suka shiga shirye-shiryen biki gadan-gadan, har ma take cewa: “Ka ga dai ranar bikinmu za mu yi kaya iri daya da kai, sannan za mu yi walima ta mata, ku maza ku ma ku yi taku ta maza. Sannan mu yi ’yan kade-kade namu na mata. Kuma zan yi wani irin kunshi da na ga kawata ta yi ranar aurenta da kitso….” (shafi na 25-6).
Ana dab da biki ne Zannira ta samu nasarar kafa kungiyar nakasassu da ma sauran mabukata don horar da hanyoyin dogaro da kai, da taimakon Yassar da abokinsa Aminu, da Amina kawar Zannira kuma budurwar Aminu. A jawabin da Yassar ya yi a wajen kaddamar da kungiyar ne yake cewa: “Ga wadanda suka san Zannira, sun san gurguwa ce, amma wannan bai hana ta neman ilimi da kuma dogaro da kanta ba, wanda wasu daga nan ne suke shiga bara da maula da sace-sace saboda mutuwar zuciya. Saboda haka ne ma ya sa ta kafa wannan kungiya ta yaki da zaman kashe wando ga maza da mata, da kuma wayar da kan jama’a bisa dogaro da kai.” (shafi na 31-2).
Muradin masoya ya samu cika, domin an daura auren Yassar da Zannira. Bayan dan lokaci da daura auren ne ma ita amaryar ta kai wa angon ziyara tare da kawarta Amina, har ma suka samu ganawa ta sirri tsakaninsu a dakinsa, domin ’yar rakiyar amaryar ba ta bi su dakin ba. Cewa ma ta yi: “Ki je kawai tun da mun gama komai, kin san ba sai ina nan ba. Kuma in muka je mu biyu sai mu dade ana ta labari. Amma in na ji shiru zan matsa ki fito mu tafi.” (shafi na 40).
Bayan sun fito, suna kan hanyar komawa gida Amina ta kara da cewa: “Kai wannan fi’ili naku da yawa yake. Da ba a yi wannan didiricin tun farko ba sai yanzu?” (shafi na 42).
Amarya Zannira ta amsa mata da cewa: “Ai da bai zama nawa ba, sai yau ya zama halak malak dina, don haka ina da damar in yi komai ba mai cewa ba nawa ne ba.” (shafi na 42).
Wannan ita ce ganawar farko kuma ta karshe ga wadannan ma’aurata, a matsayin miji da mata. Daga ita ba su sake ganin fuskar juna ba, sai dai a Daras Salamu. Domin ba su dade da rabuwa ba Yassar ya je sayayya wani kanti, wajen ketare titi mota ta buge shi, aka dauke shi zuwa asibiti. Amma kaddara ta riga fata, domin likitan da ya duba shi cewa ya yi da waliyyansa: “’Yan uwa sai dai ku yi hakuri, wannan bawan Allah rai ya yi halinsa, sai dai mu yi masa fatan rahamar Ubangiji!” (shafi na 45).
Tun bayan kwana Arba’in da rasuwar Yassar, Zannira ta fara jin canji a jikinta. Kasala da rashin jin dadin jiki suka aure ta, al’amarin da ya ki ci ya ki cinyewa, har Aminu, aminin marigayi mijinta da suke aiki tare a ofishin kungiyar da ta kafa ta horar da nakasassu, ya ba ta shawarar zuwa asibiti don auna lafiyarta. Sakamakon bincike ya fito da bayanin cewa juna biyu gare ta, kamar yadda likita ya yi wa Aminu bayani: “Yallabai ina taya ka murna, mai dakinka tana da ciki wata uku.” (Shafi na 63).
Wannan bayyanar ciki ga Zannira ya haifar da tsegunguma sosai, inda kusan kowa ya dora zargin cewa abokin aikinta a ofishinsu na kungiyar horar da sana’o’i, kuma babban aminin marigayi mijinta wato Aminu shi ne ya yi mata cikin, saboda irin matsanancin kusancin da ke tsakaninsu, domin kusan koyaushe suna tare. Sai dai kash! Ba Aminu ne ya kashe zomon ba, rataya aka ba shi, ya kuwa rike amanar da aka bar masa. Domin da gumu tai gumu, Zannira ta fuskanci matsi daga ko’ina, a karshe ta bayyana wa mahifiyarta wanda ke da alhakin cikin da take da shi, inda ta ce mata: “Ni in ban da mijina ban taba sanin wani da namiji ba.” (shafi na 70).
Samun wannan ikirari na Zannira ya sa iyayenta suka shaida wa iyayen marigayi mijinta Yassar halin da ake ciki. Nan fa sabuwar kura ta tashi, suka ce atafau ba su san wannan batu ba, inda nan take kakarsa Inna Mai Koko ta ce: “Duk mun ji bayaninku amma ba mu gamsu cewa wannan yaron ne ya yi mata ciki ba, don haka kawai wannan magana a bar ta tun rai da zumunci ba su baci ba. Yadda kuka kirkiro wannan shafa labari, ku tattara shi ku binne shi iya mu da ku kawai, kada ma wani ya ji har ya dorar, daga nan a dinga yamadidi da shi, bayan kuma bakandamiyar Bamaguje ce, wane ya ji daga wane!” (shafi na 73).
Za mu ci gaba