✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ba na yin barci a bakin aiki – Buhari

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya mayar da martani ga Bishop din Yola Rabaran Stephen Mamza wanda wanda ya ce ci gaba da kashe-kashen da ake…

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya mayar da martani ga Bishop din Yola Rabaran Stephen Mamza wanda wanda ya ce ci gaba da kashe-kashen da ake yi a kasar wata manuniya ce kan “yadda Shugaban yake barci a bakin aikinsa.”

Shugaban ya mayar da martanin ne ta bakin Babban Mai taimaka masa a fannin watsa labarai Malam Garba Shehu a ranar Litinin.

A lokacin wa’azinsa na bikin Ista, Bishop Mamza, ya soki gwamnatin Buhari kan yadda ta kasa kawo karshen kashe-kashe da satar mutane don neman kudin fansa.

Garba Shehu ya wallafa a shafinsa na Facebook cewa Babban Limamin Katolika na Yola bai yi wa Shugaba Buhari adalci ba, inda ya ce “An samu ci gaba sosai a shekara uku zuwa hudu da suka gabata a ciki da wajen garin Yola.”

Ya ci gaba da cewa: “Wannan ci gaban da aka samu ba zai yiwu ba, in da a ce Shugaban barci yake yi.” Kamar yadda BBC ya ruwaito.

Ya ce “Kimainin ’yan gudun hijira dubu 400, da ke samun mafaka a Adamawa yanzu sun koma Borno – abin da ya sa aka samu dimbin fitowar masu kada kuri’a a yankin Arewa maso Gabas lokacin zabe.”

Har ila yau ya ce: “Bayan haka garuruwan Michika da Madagali da Mubi da a baya suke karkashin ikon Boko Haram, tuni suka dawo hannun dakarun sojin Najeriya.”

A karshe Malam Garba Shehu ya ce “yankin Arewa maso Gabashin kasar ya samu ci gaba fiye da yadda yake a lokacin gwamnatin baya.”