Wanda ake zargi da kisan budurwarsa, Ummulkusum Buhari, Ummita, Mista Frank Geng, ya shaida wa kotu cewa ba ya cikin hayyacinsa lokacin da ta rasu.
Ya ce tun daga lokacin da ya janye ba ta kudi ta daina kula shi, ta ce dole ya nemi wani aiki da zai rika samun kudi sosai.
- Mutumin da ya yi wa uwa fyade a gaban ’yarta ya shiga hannu
- Dan China ya yi ikirarin kashe wa marigayiya Ummita miliyan 60
“Sai ta aiko min sako ta Whatsapp cewa ta samu sabon saurayi har ta turo min da hotunan da suka dauka tare, abin da ya bakanta min rai, musamman da na ga sun dauki hoton a cikin motar da na saya mata,” in ji shi.
Mista Geng ya ce a ranar 14 zuwa 15 ga watan Satumba marigayiyar ta ki daukar wayarsa, ko amsa sakonnin tes da ya tura mata, washegari da misalin karfe 8:30 sai ya je gidansu Ummita amma ta ki kula shi.
“Kafin na je gidan sai da na fara kiran ta a waya inda ta ce na mayar mata dan karenta (Charlie), hakan ya sa na tafi gidansu ana ruwa mai karfi a lokacin, inda na yi ta buga kofar suka ki budewa.
“Sai daga baya kanwarta ta zo ta bude sannan ta dauke karen ta shige da shi cikin gida ta bar ni a tsaye a cikin ruwan sama.
“Hakan ya sa na ci gaba da buga gidan har wani makawabcinsu, Mustapha, ya zo ya yi min magana cewa zai kirawo su su bude min kofa. Amma da ya yi musu waya bai same su ba.
“Na ci gaba da bugawa har mahaifiyarta ta zo ta bude inda na shiga gidan na dauki Charlie a kafadata na juya zan fice daga gidan.
“Sai Ummita ta fito daga falo da sauri ta kulle kofar gidan ta fara zagi na har ta mare ni; mahaifiyarta ta nemi ta daina amma ta ki sauraren ta, ta ci gaba.
“Ba shi ne karon farko da take mari na ba; ta taba mari na a gaban ’yan gidansu da kuma wani lokaci a gaban kanwarta a gidan abinci Gusto, kasancewarta mai saurin fushi; ko mutanen gidansu sun san halinta na saurin fushi.
“A lokacin ina tsaye a gidan na rasa abin yi saboda ta kulle kofar gidan.
“Daga nan cikin fushi sai ta koma daki ta dauki wuka, hakan ya sa na ji tsoro na ajiye Charlie, na yi kokari na kwace wukar a hannunta.
“Daga nan sai ta fara kokawa, muka fara kokawa inda ta cije ni a hannu da yatsuna, sannan ta rike min gabana sannan ta rika ja na cikin daki, saboda radadin da nake ji sai na bi ta.
“Duk da mahaifiyarta na yi mata tsawa ta bari amma ta ki.
“Sai ta sa kanwarta ta kira ’yan sanda wai zan yi mata fyade kuma za ta kira ’yan immigration su kama ni, daga nan sai ta tura ni kan gado ta ci gaba da zagi na.
“A wannan lokacin ne tabarauna ya bata kuma kasancewar ba na gani sosai idan ba tare da tabarau ba, ga kuma dakin fitilarsa ba ta da haske sosai, ban san yadda aka yi abin da ya faru ya faru ba.”
A cewarsa, “Sai bayan kwana uku wani Aminu ya gaya min labarin rasuwar marigayiyar. Na ji bakin cikin rasuwarta. Abu ne maras dadi.”
Lauyan wanda ake zargi, Barista Danazumi ya shaida wa kotun cewa suna da cikakkun hujjoji da za su gamsar da kotun.
Shi kuma lauyan gwamnati, Kwamishinan Shari’a na Jihar Kano, Barista Musa Abdullahi Lawan, ya nemi kotun ta dage shari’ar zuwa wani lokaci.
Alkalin kotun Mai Shari’a Sanusi Ado Ma’aji ya dage shari’ar zuwa ranar 7 da 8 ga watan Fabrairu, 2023.