✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ba na bukatar a kubutar da ni a hannun ‘yan Boko Haram- Tsohon mai yi wa kasa hidima

Wani tsohon mai yi wa kasa hidima, NYSC, mai suna Abraham Amuta, an bayar da rahoton cewa ranar Lahadi, ya ki tayin da Boko Haram…

Wani tsohon mai yi wa kasa hidima, NYSC, mai suna Abraham Amuta, an bayar da rahoton cewa ranar Lahadi, ya ki tayin da Boko Haram ta yi masa na su sako shi daga inda suke garkuwa da shi domin ya koma gida.

Maimakon haka, sai ya fada wa wadanda suka je dajin Sambisa domin kubutar da shi da su koma gida, kuma ya ma bar addininsa na Kirista zuwa Musulunci.

Amuta, wanda dan jihar Benuwe ne, an sace shi yayin da yake yi wa kasa hidima NYSC a Jihar Borno tare da wani dattijo dan shekara 58 mai suna Moses Oyekele, da wasu mutane daban a ranar 10 ga watan Afirilun bara.

An yi garkuwa da su ne, a kan hanyar Gwoza daga birnin Maiduguri, yayin da suke kokarin zuwa garin Chibok domin raba kayan agaji.

Wata bakwai bayan sace su da aka yi ‘yan Boko Haram din masu biyayya ga bangaren Abubakar Shekau, sun sako Pastor Oyekele a watan Nuwamban bara.

Aminiya ta fahimci cewa, tattaunawar da aka yi ta yi domin ganin an sako Amuta, tare da sauran wadanda suke hannun ‘yan Boko Haram din ta ruguje a ranar Lahadi, a daidai lokacin da Amuta ya yanke shawarar ci gaba da kasancewa tare da ‘yan Boko Haram din.