Dokta Innocent Okuku shi ne Shugaban Sashen Kasuwanci na Kamfanin Notore Chemical Plc da ke Najeriya. Kamfanin ne yake samar da mafi ingancin takin zamani na Uriya a duk fadin kasar nan. A wannan hira da ya yi, ya tabo batutuwa da dama da suka hada da matsalolin da manoma ke fuskanta saboda rashin samun rance don yin noma da hakan ke shafar kokarin wadata kasa da abinci. Ga yadda hirar ta kasance:
Kamar kowace irin sana’a, harkar noma tana bukatar a zuba mata jari. A ganina me manoma suka fi bukata a yanzu?
A gaskiya har yanzu ba a zuba jari ma’ana kashe kudi a bangaren yin noma a Najeriya kamar yadda ake yi a wasu sassan duniya. Idan zan iya tunawa, har yanzu bankuna a Najeriya suna bayar da rancen yin noma ne a tsakanin kashi 3 ko hudu daga kudin shigarsu. Idan aka yi la’akari da yadda fiye da kashi 60 na al’ummar kasar nan sun rungumi harkar noma ne da kuma yadda harkar ke samar da ayyukan yi ga miliyoyin ’yan kasa amma a ce bankuna suna ware kashi 3 ko 4 ne don bayar da rance ga manoma, akwai bukatar yin gyara a game da haka. Don haka yadda ake bayar da rance don yin noma a kasar nan ya zama abin takaici. Don haka kashe kudi a harkar noma ya kunshi abubuwa da dama, kama tun daga matakin yin noma da suka kunshi amfani da takin zamani da irin shuka da kuma na’urorin yin noma irin na zamani. Don haka akwai bukatar duk mai son yin noma ya yi kokarin samun filin yin noma a garinsu, don kaucewa matsalar idan ya koma wani waje ko wata jiha da ba tasa ba zai iya fuskantar matsala wajen samun filin da zai yi noma. Sai dai idan mutum yana da halin da zai iya sayen fili a can ko neman aro, ka ga ba kowane ne ke da halin yin haka ba. Ka da duk wadannan abubuwa suna bukatar kudi. Sannan bayan an yi noman, manomi yana bukatar kudi a wajen yin girbi da sauransu, duk wadannan abubuwa suna bukatar kudi. Akwai rahoton ya nuna manoma a Najeriya na asarar kayayyakin amfanin gonakinsu na akalla kashi 40 daga cikin 100 saboda rashin samun na’urorin yin noma irin na zamani don adana amfanin gonaki na lokaci mai tsawo ba tare da sun lalace ba. Don haka akwai bukatar a bullo da tsarin bayar da rance ga manoma don su samu sukunin sayen na’urorin zamani da za su yi amfani da su wajen yin shuka da girbi da kuma adana amfanin gonakinsu. Sannan hatta a bangaren sayar da amfanin gona, shi ma ana bukatar makudan kudi. Idan ka kwatanta amfanin gonar da ake shigo da su daga kasashen waje da kuma namu na cikin gida, za ka tarar nasu ya fi namu inganci saboda yadda suke amfani da na’urorin zamani wajen yin noma. Don haka idan ka dubi harkar noma daga farkonta har zuwa karshe tana bukatar sai an kashe makudan kudi.
A ra’ayinka kana ganin bankunan kasuwanci a Najeriya suna da niyyar ba manoma rance don bunkasa harkar noma?
A ra’ayina ba su da niyyar yin haka. Bankunan kasuwanci a Najeriya ba su mayar da hankali wajen bunkasa harkar noma ta hanyar ba manoma rance ba. Zan fada maka dalilin da ya sa na fadi haka.. Dalili na farko shi ne irin wadannan bankuna sun gwammace su zuba jari a bangaren man fetur da na iskar gas da harkar gine-gine. Sun gwammace su kashe kudinsu a irin wadancan bangare ne don samun “kazamar riba” maimakon zuba jari a harkar noma. Na biyu, da yawa daga cikin irin wadannan bankuna ba su fahimci alherin da ke cikin harkar noma ba. Da yawansu ba su san yadda ake yin noma ba kuma hakan ce ta sa suka ganinta a matsayin wata harka ce mai hadari. Hakan ta sa suka gwammace su karkata akalarsu a bangaren man fetur da iskar gas da kuma gine-gine. Wadannan su ne dalilan da suka sa bankunan suka yi biris wajen zuba jari a bangaren noma.
Ba ka ganin ya kamata a lura da tsarin gwamnati, domin idan ana da tsarin da ke tilasta bankuna domin su bayar da isashen bashi ga noma, wannan ba zai taimaka ba wurin kara samun tallafi a harkar?
Na yarda. Ina nufin idan tsarin gwamnati ya tilasta bankuna su bayar da rance ga noma- idan ka tambaye ni kamar kashi nawa nake gani, kamar kashi Ashirin da biyar saboda abinda muke bukata a yanzu shi ne komawa ga harkar noma kuma harkar na bukatar kudi sosai; sannan idan ana bukatar taimakon bankunan mu, yadda za a yi shi ne a tabbatar cewa ba ya kasa da kashi daya bisa hudu na abin da suke warewa domin bayar da rance a harkar noma. Idan gwamnati ta tilasta hakan, to za mu samu isassun kudin da za a rika warewa don yin noma. Amma kuma ba wai kawai su bayar da kashi kaza ba, wani abun shi ne a duba ko suna da damar bayarwar kuma su lura da abin da suka bayar zuwa ga harkar yadda yakamata ta yadda za su samu damar karbar kudinsu daga baya. Saboda idan na bada Naira biliyan biyu a misali ga harkar noma kamar a ce kashi Ashirin da biyar na abin da nake bayarwa a wannan lokacin, idan ban samu damar karbo wadannan kudaden ba, ban da damar bayar da wani kudin nan gaba, misali idan banki ne. Don haka, ba wai kawai a ce na bayar da bashin kudin da ya kai yawa kaza ba, ya kamata a taimaka mini ko kuma a kara karfafani ta yadda zan iya lura da duk abin da na bai wa harkar noma.
Idan ka lura da yanayin ma’aikatan banki a yau, kadan daga cikin su ne suka san mene ne harkar noma, don haka bankuna suna bukatar masana a harkar ta noma wadanda suka san aikin noman, su shigo cikin harkar a dama da su sannan sai su hada kwarewarsu ta harkar noman da kuma kwarewarsu a harkar banki sannan sai su zo da hanya mafi dacewa wurin bayar da bashi ga manoma. Dan haka na yadda tsarin gwamnati ya tilasta a kara yawan ba ma manoma bashi.
Ko ka yi amanna da cewa ya dace a zuba kudi ta bangaren kayan aikin noma?
kwarai kuwa, ya zama wajibi a zuba kudi a bangaren domin kuwa kayan aikin noma kaya ne na musamman. Misali, ba kamar mutum ba ne ya ce zai je bakin titi ya sayi mota, duk kuwa da cewa kayan aikin noma ba su cika lalacewa da wuri ba, suna da juriya. Idan ka dauki misali kamar irin shuka, shi irin shuka yana rage inganci ne idan ya dauki lokaci a ajiye, don haka kudin da za a tallafa ya kamata su kasance a lokacin da ya dace. Muna bukatar mu shirya wani tsari wanda ya dace, yadda za a samar da kudin, ta yadda manoma za su same su a lokacin da ya dace da su, domin su samu kayan aikin noma a farashin da ya dace.
Abin da ya kamata kuma mu fahimta shi ne, wani lokaci, al’amarin ba na matsalar samun kudin ba ne, amma matsalar inda take shi ne, wasu manoman ba su da amanna kan abin da suka sanya gaba, misali noma. Idan sun samu kudin, ba su da amannar cewa lallai za su yi noma da su har su samu abin da suke bukata daga gare su.
Akwai dillalan kayan noma da suka kasa biyan basussukan da suka amsa daga bankuna saboda gwamnati ta rike masu kudade masu yawa da suke bin ta. Ba ka ganin cewa wannan zai gurgunta tsarin ba da rancen noma daga bankuna?
Abin da ya kamata a fahimta shi ne, ita gwamnati idan ta ce za ta sanya hannunta kan wata harka, za ta yi ne da nufin bunkasa harkar, domin a samu saurin ci gaba, ba za ta kawo tsarin da zai rikita harkar ba. Idan misali ka ce kana son gwamnati ta taimaki manoma yadda za su rika samun kayan aikin noma cikin sauki ta hanyar taimakon dillalan kayan aikin noma, to sai a duba tsarin da dillalan suke kai, sai a inganta shi. Idan idan ka ce za ka fita daga hurumin tsarin da dillalan suke, ka ce za ka yi mu’amala da wadanda ba su da tsari, ba su da sanayya da abokan hulda, wannan zai haifar da babbar matsala. Kuma ka sani, su bankuna suna tantancewa sosai ga wadanda suke ba rance, domin gudun kada su ba bara-gurbi kudi, sai sun samu tabbacin cewa kudadensu za su dawo. Na sha samun labarai daban-daban, inda wasu da dama daga dillalan nan, ba su amfani da kudaden da suka ranta yadda ya kamata. Ya zuwa yanzu gwamnati na batun fara biyansu, amma abin da ma ya kamata a duba shi ne, kudaden da dillalan ke bin gwamnati, ko kadan ba su kai yawan adadin da bankuna ke bin su ba. Don haka ko gwamnati ta biya su, ba za su iya biyan bashin da suka ci daga bankuna ba, domin kuwa tun da farko sun karkatar da kudaden ne zuwa wata harka daban.
Ko kana kira da a ware wasu kudin musamman don samar da iri da kayan noma?
Eh. Tabbas saboda iri da kayan noma abubuwa ne da suka bambanta da sauran kayan da ake amfani da su yau da kullum. Su ba kamar motar hawa ba ne da mutum zai je ya saya kai-tsaye. Abin farko shi ne, su suna lalacewa kuma tasirin iri yana raguwa idan ya dade a ajiye. Wannan ya sa akwai bukatar a kashe kudi a kansu a lokacin da ya dace, akwai lokacin da ake bukatar hakan, amma ba kowane lokaci ba. Saboda haka kaya ne da suka bambanta da saura.
Ya kamata mu fito da wani tsari wanda za a ware wasu kudi don samar da iri da kayan noma saboda manoma su same su a cikin rahusa kuma a kan lokaci. Amma tambayar ita ce ko ya dace a rage farashin kayan noma, ko kuma a samar da tallafi saboda a wadata manoma da ingantattun kayan noma musamman domin sun san idan suka yi amfani da irin wadannan kayan, amfanin gonarsu zai karbu a kasuwa. Misali gwamnati za ta iya fito da wani shiri da zai tabbatar da samar da kayan cikin rahusa. Idan na noma shinkafa misali, nasan cewa duk kunci zan sayar da buhu guda akalla a kan Naira dubu takwas. Ba tare da la’akari da farashin ba, saboda idan aka kai amfanin kasuwa kuma ana tayawa kasa da yadda ya dace, akwai wani wuri da gwamnati ta tanada inda zan sayar a kan dubu takwas kuma nasan a haka za a fita. Saboda hakan zan kashe kudi wajen irin da kuma kayan noman da suka dace don samun amfanin shinkafar mai yawa. Amma idan kuma ina da tunanin cewa bayan na noma shinkafa da yawa, zan kai kasuwa a taya mini buhu Naira dubu biyar, hakan yana nufin zan fadi ke nan, to ka ga ba zan ji tsoron sanya kudi sosai a harkar. A wasu lokuta samar da kudin ba shi yake da wahala ba, amma rashin tabbas da manoma suke da shi kan ko za su mayar da riba da uwar kudi.
Ya ku masu karatu, ko kuna da wata tambaya da ta danganci kowace irin matsalar noma da kiwo? Ko kuwa kuna bukatar wani bayani game da takin zamani? Kuna iya aiko da tambayoyinku ko bayananku ta adireshinmu na I-Mel: [email protected]