Jakadan kasar Kenya a Najeriya, Wilfred Machage, ya musanta labarin da ake yadawa kan hannun kasarsa a cafke shugaban ’yan awaren Biyafara na IPOB, Nnamdi Kanu.
Hakan na zuwa ne bayan dan uwan Kanun, Kingsley Kalu a ranar Laraba ya yi zargin cewar an cafke dan uwan nasa ne a kasar ta Kenya.
- Yawan mutanen da COVID-19 ta kashe a Indiya sun haura 400,000
- Tallafin Mai zai iya lashe N900bn a 2022 – Minista
“Bayan Nnamdi Kanu ya ziyarci Kenya jami’an tsaro sun cafke sannan suka mika shi ga hukumomin Najeriya, su kuma suka dawo da shi,” a cewarsa.
Sai dai da yake ganawa da manema labarai a Abuja ranar Juma’a, Ambasada Machage ya ce “Ina so na kalubalanci duk wanda ya ce a Kenya aka kama shi da ya gabatar da hujja.
“Su zo su fada mana yaushe, ina da kuma su waye suka kama shi,” inji jakadan.
Ya ce zargin a matsayin labarin kanzon-kurege don a fusata wasu mutane na daban.
Ya ce Kenya a matsayinta na kasa ta yi mamakin jawabin da aka fitar a jaridu cewar an cafke shi a can.
Kazalika, shugaban Hukumar Shige da Fice ta Kasar ta Kenya, Alexander Muteshi, shima ya musanta labarin.
Kama Nnamdi Kanun da aka yi dai ya karade kafafen watsa labarai a Najeriya, sai dai Gwamnatin Najeriya ta ja bakinta ta yi gum kan inda ta kamo shi.