✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

B/Haram ta kashe mutum 30 a gidan kallon kwallo a Borno

A kalla matasa 30 masu kallon kwallo  a kauyen Mandarari da ke Karamar Hukumar Konduga a Jihar Borno ne suka rasu, yayin da sama da…

A kalla matasa 30 masu kallon kwallo  a kauyen Mandarari da ke Karamar Hukumar Konduga a Jihar Borno ne suka rasu, yayin da sama da 40 suka ji mummunan raunuka a wani harin kunar bakin waken da ake zaton ’ya’yan kungiyar Boko Haram ne suka kai a Lahadin da ta gabata da dare. Garin Konduga mai tazarar kilomita 36 daga birnin Maiduguri  ya sha fama da irin wadannan hare-hare daga  kungiyar Boko Haram a baya.

Bayanai sun ce maharan su 3 ne, mata biyu da namiji daya sun kai harin ne a daidai lokacin da masoya kallon kwallon kafa suka cika makil a wani shagon kallon kwallo a Mandarari.

Babu zato sai suka tayar da bama-bamai da ya yi sanadiyyar hallaka akalla mutum 30 yayin da wadansu 40 suka ji munanan raunuka wadanda suke kwance a Asibitin Kwararru na Maiduguri suna jinya.

Wani wanda abin ya rutsa da shi kuma a yanzu yake kwance a gadon asibiti mai suna Bukar Modu, ya shaida wa wakilinmu cewa, “A ranar Lahadi da misalin karfe  9 na dare, muna kallon kwallon kasasnen waje, muna shewa domin kungiyar da muke so ita ke kokari a lokacin, duk hankalinmu ya koma kan talabijin sai muka ji karar tashin bam, tun daga nan ban san halin da nake ciki ba sai kawai na iske kaina a gadon asibiti. A da ba na iya magana, amma yanzu ga shi har hira muka yi da kai, alhamdulillah.”

Hukumar Bayar Da  Agajin Gaggawa ta Kasa (NEMA) ta tabbatar da aukuwar al’amarin ta bakin kakakinta, Malam Abdulkadir Ibrahim.