✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Azumi na gaskiya (1)

Daga Hudubar Sheikh Abdulbari bin Iwad As-Sabitiy Masallacin Annabi, Madina Huduba ta Farko Godiya da hamdala ga Allah.Bayan haka, ku bi Allah da takawa a…

Daga Hudubar Sheikh Abdulbari bin Iwad As-Sabitiy

Masallacin Annabi, Madina

Huduba ta Farko

Godiya da hamdala ga Allah.
Bayan haka, ku bi Allah da takawa a kan hakkin binSa da takawa, Allah Madaukaki Ya ce: “Ya ku wadanda suka yi imani! Ku bi Allah da takawa a kan hakkin binSa, kuma kada ku mutu face kuna masu sallamawa (Musulmi)” (k:3:102).
Ranaku suna shudewa kamar shudewar girgije, shekaru suna wucewa da sauri, alhali muna cikin mayen rayuwa muna shagaltattu. ’Yan kadan ne suke tunani kan halin da muke ciki ko makomarmu. Allah Madaukaki Ya ce: “Kuma Shi ne Wanda Ya sanya dare da yini a kan mayewa, ga wanda yake son ya yi tunani, ko kuwa ya yi nufin ya gode.” (k:25:62).
Musulmi a cikin shekarunsa abin iyakancewa ne, kuma rayuwarsa gajera ce. Hakika Allah Ya sanya masa wasu ayyukan musamman na alheri, kuma Ya ba shi daga zamani da wuri masu daraja da za su kange shi daga karkacewa su daidaita rayuwarsa. Daga cikin wadannan ayyuka akwai azumin watan Ramadan Mai albarka. Allah Madaukaki Ya ce: “Ya ku wadanda suka yi imani! An wajabta azumi a kanku kamar yadda aka wajabta shi a kan wadanda suke gabaninku, tsammaninku za ku yi takawa.” (k:2:183).
A cikin watan Ramadan takun sha’awoyi kan ragu a cikin zukatan da suke da imani. Ayyukan kankan da kai su daukaka a cikin yini da dare. Wani yana rokon afuwa kan gazawarsa, wani yana rokon dacewa a cikin ayyukan da’arsa, wani kuma yana isti’aza daga ukuba, wani yana fatar kyakkyawar lada, wani kuma zikiri ya shagaltar da shi. Tsarki ya tabbata ga Wanda Ya datar da su, yayin da aka haramta hakan ga wasunsu.
Watan Ramadan wata ne na karfi da kyauta, wata ne na raya dare da imani, wata ne na aiki da hakuri, ba wata ne na rauni da kasala da barci ba. Kasalar wasu masu azumi da komawarsu ga barci a wuninsa da karanta ayyukan da’a sun saba wa hikimar yin azumi, ba su dace da manufarsa ba.
Musulmin farko sun kasance suna rayuwa ne a cikin Ramadan da zukatansu da hankalinsu, idan dayansu na azumi, hakika yana kiyaye wuninsa yana mai hakuri kan wahalhalu, yana kiyaye dokokin Allah da jin tsoronSa. Mai nesa da duk abin da zai bata wuninsa ya bata azuminsa. Ba ya furta mummunar magana, kuma ba ya fadin komai sai alheri, ko ya yi shiru. Kuma darensa ya kasance yana kashe shi ne cikin Sallah da tilawar Alkur’ani da zikiri domin koyi da Manzon Allah (SAW).
Ribar azumi da sakamako da falalarsa ba su da iyaka, kidaya ba ta kididdige su, sai dai ba a sanya masu kasala a ciki, masu wasa da suke bata watan wajen barci, ko shafe dare a rumfunan kasuwanci da kashe dare ana wasa da shagala.
Azumi garkuwa ne daga wuta kamar yadda Ahmad ya ruwaito daga Jabir (RA) cewa: “Lallai Annabi (SAW) ya ce: “Abin sani azumi garkuwa ne daga wuta.” Azumi garkuwa ne daga sha’awoyi, domin hakika ya zo a cikin Hadisin Ibnu Mas’ud (RA) cewa: “Lallai Annabi (SAW) ya ce: “Ya ku taron samari! Wanda yake da ikon yin aure daga cikinku, to ya yi aure, domin shi ne mafi sanya runtse idanu, kuma mafi tsaron farji (daga zina); wanda ba ya da ikon yin auren kuwa, to ya yi azumi, “saboda shi dandaka ne.” Buhari da Muslim suka ruwaito.
Azumi hanya ce ta zuwa Aljanna, Nisa’i ya ruwaito daga Abu Amama ya ce: “Na zo ga Manzon Allah (SAW) na ce: “Ka umarce ni da wani al’amari da zan rike daga gare ka.” Sai ya ce: “Na hore ka da yin azumi, domin babu kamarsa.”
An karbo daga Sahlu bin Sa’ad (RA) cewa: “Lallai Annabi (SAW) ya ce: “Lallai a cikin Aljanna akwai wata kofa ana ce da ita: Rayyan. Masu azumi ne za su shiga ta ita a Ranar kiyama, babu mai shiga ta cikinta bayan su. Za a rika cewa ina masu azumi? Sai su tashi, babu mai shiga ta cikinta sai su. Idan suka shiga sai a kulle, babu mai shiga a bayansu.” Buhari da Muslim suka ruwaito.
Imam Ahmad ya ruwaito daga Abdullahi bin Amru bin Al-As (RA) cewa: “Lallai Annabi (SAW) ya ce: “Azumi da Alkur’ani suna ceton bawa a Ranar kiyama. Azumi zai ce: “Ya Ubangiji! Na hana shi abinci da sha’awoyi da rana, Ka ba ni cetonsa. Alkur’ani kuma ya ce: “Na hana shi barci cikin dare, Ka ba ni cetonsa. Ya ce: “Sai su (biyun) su cece su.”
Azumi kaffara ce da gafara ga zunubai, domin kyawawan ayyuka suna kankare munana. Hakika (SAW) ya ce a Hadisin Abu Huraira (RA): “Wanda ya yi azumi yana mai imani da neman lada, (ikhlasi) an gafarta masa abin da ya gabata na zunubinsa.”
Azumi sababi ne na samun sa’ada a duniya da Lahira. Manzon Allah (SAW) ya fadi a Hadisin Abu Huraira cewa: “Na rantse da wanda ran Annabi Muhammad ke hannunSa, warin bakin mai azumi ya fi soyuwa a wurin Allah daga kanshin turaren almiski. Kuma mai azumi yana da farin ciki biyu: idan ya yi buda-baki da kuma in ya hadu da Ubangijinsa, zai yi farin ciki da azuminsa.” Buhari da Muslim suka ruwaito.
Shin za mu sanya wa Ramadan wani lokaci ya zama na komawa ga Allah da hisabi ga kai da kyautata inda muka gaza a bangaren Allah? Shin ko daliban ilimi da masu da’awa za su sanya Ramadan ya zama wani lokaci na jaddada himma da tsarkake niyya? Ko kuwa Ramadan zai kasance wata fursa ce da kowane Musulmi zai taimaki dan uwansa azzalumi ko wanda aka zalunta, ya taimaki wanda ake zalunta ta hanyar kwato masa abin da aka zalunce shi, ya taimaki azzalumi ta hana shi yin zaluncin, har sai mutanen kirki su shugabanci al’ummar Musulmi? Ko kuwa Ramadan zai kasance wata fursa ga mawadata su warware bukatun fakirai, su yi shukura kan ni’imar da aka yi musu ta hanyar ajiye ta a inda Wanda Ya ba su ni’imar Ya ce, ta yadda za su iya ceto mayunwata daga cikin al’ummar Musulmi, wadanda imaninsu yana iya fadawa ga hadari, idan suka gaza ciyar da mayunwatan cikinsu ko tufatar da marasa tufafinsu ko shayar da masu jin kishinsu? Ko kuwa Ramadan zai kasance wani lokaci da kowane Musulmi zai fahimci kasala da rashin kazar-kazar na iya jefa shi ga aikata kaba’ira, ta yadda zai ciru daga giba da annamimanci da mugun zato da wulakanci da raina dan uwansa Musulmi?
Ya ku bayin Allah! Ramadan babbar makaranta ce da muke samun horo a darensa da wuninsa, gabobinmu su karfafa da shiftarsa har sai sun yi kamar yadda Ubangiji Mahaliccinsu Ya yi nufi. Ya zo a cikin Hadisin kudusi cewa: “BawaNa ba zai gushe yana kusantaTa da nafilfili ba, har sai Na so shi. Idan kuma Na so shi, sai in kasance jinsa da yake ji da shi da ganinsa da yake gani da shi da hannunsa da yake damka da shi da kafarsa da yake tafiya da ita.” Buhari ya ruwaito.
Makarantar azumi tana tarbiyyantarwa kan karfi da gaskiyar niyya. Wadannan su ne ke karya turakun son zuciya, su mayar da igiyoyin sharri. Duk wani karfi ko tsari zai yi wuya ga mumini daga mafitar rana zuwa mafadarta yana ci abinci ko abin sha na wani lokaci. Za a ga yana rike da akalar rayuwarsa yana hana ta fadawa ga sha’awoyi ko abubuwan son zuciya. Kai yana iya ce da zuciyarsa na ki. Me ya fi dadi a ce ta kasance cikin neman yardar Allah. Ba ta jima’i da rana ba ta fasikanci. Kuma da jahili zai bata mata ya nemi tayar da hankalinta, zai ya yi linzami ga fisgar sharri da fadi da cewa: “Ni mai azumi ne!”
Azumi na gaskiya yana tsarkake zuciya daga miyagun kullace-kullace da zunubai da sharruka. Yana kange harsuna daga furta maganganun banza da hana ido ganin haram.
Amma daga cikin masu azumi akwai mai azumin da ba ya da komai sai yunwa da kishin ruwa. Domin mutumin da ke barin abinci, amma ya ci naman ’yan uwansa da giba, yana kamewa daga abin sha, amma bai kamewa daga karya da algushu da zaluntar mutane, yunwa da kishin banza yake sha.
Azumi na gaskiya yana sa Musulmi ya zama mai faffadar zuciya, mai tattausan harshe, ya zamo mafi gudu daga husuma da sharri, idan aka yi masa laifi ko aka munanta masa ya yi hakuri. “Masu hakuri kawai ake cika wa ijararsu, ba da wani lissafi ba.” (k:39:10).