✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Azumi da hukunce-hukuncensa (2)

Daga Umar Ahmed ’Yanleman Sannan an samu wannan nassi a cikin Muwadda Malik. Kuma Yazid bin Ruman ya ce, mutane sukan yi raka’a 23 a…

Daga Umar Ahmed ’Yanleman

Sannan an samu wannan nassi a cikin Muwadda Malik. Kuma Yazid bin Ruman ya ce, mutane sukan yi raka’a 23 a zamani Umar (RA). Raka’a 20 na Tarwihi uku na Shafa’i da Wutri,
Malik ya ce, “Za a iya Sallar Tarawihi raka’a 30 da shida ban da Wutri. Ya kafa hujja da cewa mutanen Madina sun gabatar da raka’a 36 a lokacin da suke Sallar Tarawihi. Nafi’u kuma ya ce, “Na hadu da mutanen da suke yi raka’a 39;” don haka kana iya yin raka’a 11 kamar yadda Manzon Allah (SAW) yake yi ko ka yi raka’a 23 kamar yadda ake yi a zamanin Umar ko ka yi raka’a 39 kamar yadda mutanen Madina suke yi
Wasu sun ce mutum zai iya raka’a takwas, idan  yana son ya jinkirta Wutri zuwa can dare. A tuna Manzon Allah (SAW) ya umarci muminai da riko da Sunnarsa da Sunnar halifofinsa shiryayyu da za su biyo bayansa.
Ya fi dacewa a yi Sallar Tarawihi a cikin jama’a, a masallaci fiye da yi a gida ko a daidaiku. Sallar Tarawihi tamkar Sallar Idi ce (karama da Babbar Sallah). Kuma daga farko sahabbai suna gabatar da Sallar Tarawihi cikin jam’i tare da Manzon Allah (SAW) ne. Sa’id ya ce, “Wata rana da dare Manzon Allah (SAW) ya gabatar da sallar kiyamur Ramadan a masallaci, sai sahabbai suka bi shi, suka yi haka a rana ta biyu da rana ta uku ta zo, sai Manzon Allah bai fito ba. Da safe sai sahabbai suka tambaye shi, sai ya ce, “Na ji lokacin da kuka taru a masallaci kuna jira na, kuma ban fito ba ne, saboda tsoron kada a mayar da ita farilla.”
Sallar Nafila da sauran ayyukan ibada a daren Lailatul kadari:
Allah Madaukaki Ya ce: “Lallai Mu, Mun saukar da shi (Alkur’ani) a cikin daren Lailatul kadari (daren daraja)” (k:97:1). Kuma Ya sake cewa: “Lallai ne Mu Muka saukar da shi a cikin wani mai albarka. Kuma lallai ne Mu, Mun kasance Masu yin gargadi.” (k:44:3).
Daren Lailatul kadari shi ne dare mafi fiffikon daraja da daukaka a tsakanin dukkan darare. Allah Yakan umarci Mala’ika Jibrilu (AS) da sauran mala’iku su sauko duniya. Dare ne mai cike da aminci da salama har zuwa wayewar gari. A daren ne Ubangiji Yakan tsara dukkan abin da zai faru ga mutane da sauran halittu na tsawon shekara. A daren yake tsara wadanda za a haifa da wadanda za su mutu da wadanda za su yi rashin lafiya da wadanda za su samu ko su yi rashi da wadanda jarrabawa za ta shafe su walau kyakkyawa ko mummuna da sauransu. Za a tsara yadda wadannan abubuwa da muka lissafo a sama za su faru a dukkan gushewar yini bayan yini da dare bayan dare da sa’a bayan sa’a da minti bayan minti da wata bayan wata da yanayi bayan yanayi. Allah Madaukaki Ya ce: “A cikinsa (daren Lailatul kadari) ake rarrabe kowane al’amari bayyananne. Umarni daga wurinMu. Lallai Mu ne Muka kasance Masu aikatawa.” (k:44:4-5).
Kuma Allah Madaukaki Ya sake cewa: “To me ya sanar da kai abin da ake kira Lailatul kadari? Lailatul kadari shi ne mafi alheri daga wasu watanni dubu, (wato yin abada domin Allah a cikinsa ya fi ibadar wata dubu wato shekara 83 da wata hudu). Mala’iku da Ruhu (Jibrilu AS) suna sauka a cikinsa da izinin Ubangijinsu saboda kowane uamrni. Salama ne shi daren har fitar alfijir.” (k:97: 2-5).
A’isha matar Manzon Allah (SAW) ta ce daga zarar goman karshe na Ramadan ya zo, Manzon Allah ya daina barci a dararen ranakun. Yana tashin matansa da ’ya’yansa, kuma a lokacin ne ya fi dagewa wajen bautar Ubangiji. A duba Buhari da Musulim. Kuma ta ce, Manzon Allah yaka tare a masallaci a goman karshe na Ramadan, kuma yakan ce “Ku nemi daren Lailatul kadari a Wutrin goman karshe na watan Ramadan.”
Abu Huraira (RA) ya ce: “Manzon Allah (SAW) ya ce: “Duk wanda ya yi sallar nafila cikin daren Lailatul kadari cikin imani da neman Allah (ikhlasi), to an gafarta masa dukkan zunubansa.” Buhari da Muslim suka ruwaito.
A’isha (RA) matar Manzon Allah (SAW) ta ce: “Manzon Allah yakan tsayu sosai wajen gudanar da ibada a watan Ramadan, amma ya fi tsayuwa sosai a goman karshe na watan Ramadan.” Muslim ya ruwaito shi. Kuma ta ce: “Manzon Allah (SAW) yakan nemi daren Lailatul kadari a wutrin (21 ko 23 ko 25 ko 27 ko 29) goman karshe na Ramadan.” Buhari ya ruwaito shi.
Ibnu Umar (RA) ya ce: “Wadansu daga cikin sahabban Manzon Allah (SAW) sun sha yin mafarkin cewa daren Lailatul kadari yana zuwa ne a bakwan karshe na watan Ramadan. Kuma Manzon Allah (SAW) ya ce: “Na ga duk mafarke-mafarkenku sun tsaya ne ga ranakun bakwan karshe na Ramadan. Don haka duk wanda yake son ya yi gamo da katar da daren Lailatul kadari sai ya nemi shi a daren ranakun bakwan karshe na Ramadan.” Buhari ya ruwaito shi.
Ittikafi:
Ittikafi a shari’a yana nufin killace kai a masallaci da niyyar kusantar Allah don gabatar da wasu ayyukan ibada. Dukkan malamai sun yarda a yi ittikafi, saboda Manzon Allah yakan tare a masallaci a ranakun goman karshe na watan Ramadan yana ibada har zuwa wafatinsa, kuma matansa da sauran muminai sun ci gaba da yin haka bayan wafatinsa.
Sharuddan yin ittikafi:
Dole ne mutum ya kasance Musulmi kafin ya yi ittikafi, kuma ya zama mukallafi, kuma ya kasance ba ya cikin janaba, ga mace kuma da karin tsarkaka daga jinin haila ko na biki.
Babban abin da ake bukata kafin ittikafi shi ne a killace kai a msallaci da niyyar kusantar Allah cikin ikhlasi.
Abubuwan da suka halatta ga mai ittikafi:
a.    Fitowa daga inda yake ittikafin don yi sallama da iyalinsa.
b.     Ya halatta ya rika taje gashin kai ko aske shi da yanke farce da yin wanka da sanya turare da kuma sanya tufafi masu kyau.
c.    Ya halatta mai ittikafi ya fita wajen masallaci domin zuwa bahaya ko cin abinci ko shan ruwa idan har babu mai kawo masa.
d.     Ya halatta mai ittikafi ya ci abinci ya sha abin sha bayan buda baki. Kuma zai iya yin barci a cikin masallaci tare da kiyaye alfarmar masallacin.
Abubuwan kiyayewa yayin ittikafi:
Bai kamata wanda ke yi ittikafi ya fita zuwa gaisar da marar lafiya ba, ko zuwa jana’iza ko saduwa da mace, ko kuma ya fita daga masallaci ba tare da dalili mai karfi ba. Babu ittikafi ga marar azumi, kuma ba a ittikafi sai a masallacin Juma’a. A duba Baihaki da Abu Dawud don karin bayani kan haka.
Abubuwan da suke bata ittikafi:
a). Fita daga masallaci ba tare da kwakkwaran dalili ba.
b). Suma ko maye ko kamuwa da ciwon hauka.
c). Zuwan jinin haila ko na biki ga mata.

Umar ’Yanleman
Cibiyar Al’adun Musulunci a Najeriya (ICCN)
Abuja
08066441995