Alkhurdabi ya ce: “Azumi sirri ne a tsakanin bawa da Ubangijinsa, babu mai gano hakikaninsa sai Shi (Allah), domin haka ya kasance kebantacce gare Shi.” (Al-Jami’u Li Ahkamil kur’an, Mujalladi na 2 shafi na 274).
Azumi da hakuri:
Baya ga takawa da kangae gabbai da sanya wad an Adam ikhlasi, azumi yana koyar da hakuri, bilhasali ma azumi wani yanki ne na hakurin kamar yadda Ibnu Rajab ya nuna: “Azumi yana daga cikin hakuri. Shi kuma hakuri nau’o’i uku ne: kuma duka nau’o’in uku sun hadu a cikin azumi. Domin a cikinsa akwai hakuri a kan yi wa Allah da’a da hakuri daga aikata abin da Allah Ya haramta ga mai azumi na abubuwan sha’awa da kuma hakuri kana bin da zai shafi mai azumi na radadin yunwa da jin kishi da wahalar da rai ke gamuwa da shi da kuma raunin gababuwa. Allah Madaukaki Ya ce: “Masu hakuri kawai ake cika wa ijararsu, ba da wani lissafi ba.” (k:39:10).” (Lada’iful Ma’arif, shafi na 284 da Mawaridul Zam’an, Mujalladi na 1 shafi na 357).
Ibnu Aiyinah ya ce: “Azumi shi ne hakuri, mutum yana hakurtar da kansa daga abinci da abin sha da jima’i. Sannan ya karanta: “Masu hakuri kawai ake cika wa ijararsu, ba da wani lissafi ba.” (k:39:10).” (Sharhu Sahihil Bukhari na Ibnu Baddal, Mujalladi na 4 shafi na 9).
Ibnu Hajri kuma ya ce: “Masu hakuri su ne masu azumi a mafi yawan maganganu.” (Fathul Bari, Mujalladi na 4, shafi na 130).
Abu Huraira (RA) ya ce: “Na ji Manzon Allah (SAW) yana cewa: “Watan hakuri da ranaku uku na kowane wata azumin shekara ne.” Suyudi ya ce: “Watan hakuri shi ne watan Ramadan. Kuma asalin hakuri shi ne kamewa, sai aka kira azumi da hakuri saboda abin da ke cikinsa na kame rai daga ci da shad a jima’i.” (Sharhu Sunani Nisa’i, Mujalladi na 4 shafi na 218).
Kuma Manzon Allah (SAW) ya ce da wani mutum: “Ka azumci watan hakuri da yini daya a kowane wata.” Sai ya ce: “Ka kara min domin ina da karfi.” Sai ya ce: “Ka azumnci yini biyu.” Sai ya ce: “Ka kara min.” Sai ya ce: Ka azumta daga masu alfarma, ka bari, ka azumta daga masu alfarma, ka bari, ka azumta daga masu alfarma, ka bari. Sai ya fadi (da nuni da) yatsunsa guda uku ya damke su sannan ya sake su.” (Abu Dawuda da Ibnu Majah da Ahmad suka ruwaito).
Alkhidabi ya ce: “Fadinsa: “Daga masu alfarma,” to lallai masu alfarma watanni hudu ne. Su ne wadanda Allah Madaukaki Ya ambata a cikin LittafinSa, inda Ya ce: “Lallai kidayar watanni a wurin Allah guda goma sha biyu ne a cikin Littafin Allah ranar da Ya halitta sammai da kasa, daga cikinsu akwai hudu masu alfarma.” (Tauba:36). Su ne watan Rajab da Zul-kida da Zul-Hajji da Muharram.” (Mu’alimus Sunani, Mujalladi na 3 shafi na 306).
Domin haka Ramadan wata makaranta ce ta koyon hakuri, shi ya sa Ibnu Rajab Alhambali ya ce: “Mafi falalar nau’o’in hakuri shi ne: Azumi, domin shi ya tara hakuri a kan abubuwa uku. Domin shi hakuri ne a ka yi wa Allah Madaukaki da’a. Sai hakuri daga saba wa Allah, domin bawa yana bari sha’awoyinsa domin Allah a lokacin da ransa ke jayayya da shi kan ya aikata shi. Saboda haka ne ya zo a cikin Hadisi ingantacce cewa lallai Allah Madaukaki Yana cewa: “Dukkan aikin dan Adam nasa ne sai dai azumi, lallai shi Nawa ne, Ni zan saka a kansa. Lallai shi ya bar sha’awoyinsa da abincinsa da abin shansa saboda Ni.” (Buhari, Babin Azumi Hadisi na 1805 da Muslim Babin Azumi, Hadisi na 1151).
Azumi da shukura ga ni’ima:
Sheikh Abdul’aziz As-Salman ya ce: “Azumi yana kira zuwa ga yin shukura ga ni’imar Allah. Domin shi kame rai ne daga abinci da abin sha da saduwa da mata. Kuma mutum ba zai san girman wadannan ni’imomi ba, sai bayan ya rasa su, sai wannan ya farkar da shi ga tsayuwa da yin shukura a kansu. Kuma zuwa ga haka ne Allah Madaukaki Ya yi ishara a cikin fadinSa: “Tsammaninku za ku yi godiya (shukura)” (Bakara: 185).
Azumi da dabi’ar karimci da tausaya wa fakirai:
Ibnu Rajab ya ce: “An tambayi wani daga cikin magabata (Salaf) don me aka shari’anta azumi?” Sai ya ce: “Domin mawadaci ya dandani yunwa ya daina mantawa da mayunwaci.” (24).
Sheikh Muhammad Rashid Rida ya ce: “Lallai lokacin da mai azumi ya ji yunwa zai tuna da wanda bai samun abinci, sai hakan ya sanya shi ya rika tausayawa da jinkai da za su sanya ra rika yawaita kyauta da sadaka. Hakika Allah Ya siffanta AnnabinSa da cewa mai tausayawa ne mai jinkai. Don haka Ya yardarm wa bayinSa muminai abin da Ya yardarm wa AnnabinSa (SAW), domin haka ne Ya umarce su da koyi da shi.” (25).
An karbo daga Ibnu Abbas (RA) ya ce: “Manzon Allah ya kasance mafi kyauta da alheri ga mutane, amma ya fi yin kyauta a cikin watan Ramadan, lokacin da Jibrila ke ganawa da shi.” (26). Zubairu bin Almunir ya ce: “Ma’ana alherinsa da kyautatawarsa (SAW) suna game mai siffar fakiranci ko mabukaci da wanda ke da siffar wadata da isa fiye da yadda girgijen da iska ke gamewa wajen saukar da ruwa.” (27).
Ibnu Hajrin ya ce: “Lallai a cikinsa akwai cewa mudarasar Alkur’ani tana jaddada alkawari wajen karin wadatar zuci. Wadatar zuci kuma sababi ne na yin kyauta. Kyauta kuma a shari’a ita ce: “Ba da abin da ya dace ga wanda ya dace. Kuma ita ta fi gamewa fiye da sadaka. Kuma har wa yau Ramadan lokaci ne na alherai, domin ni’imar Allah a kan bayinSa a cikinsa tana karuwa a kan waninsa…..” (Fathul Bari, Mujalladi na 1 shafi na 31).
Hanyoyin yin kyauta da kyautatawa:
1. Ciyar da mai azumi:
An karbo daga Zaidu bin Khalid Al-Juhni ya ce: “Manzon Allah (SAW) ya ce: “Wanda ya ciyar da mai azumi yana da lada gwargwadon ladarsa (mai azumin) ba tare da an rage wani abu daga ladan mai azumin ba.” (Tirmizi, Hadisi na 807 da Ibnu Majah, Hadisi na 1746, kuma Tirmizi ya ce: “Wannan Hadisi ne mai kyau ingantacce).
2. Kyautata wa iyaye da sadar da zumunta:
An karbo daga Abu Huraira (RA) ya ce: “Wani mutum ya zo wurin Manzon Allah (SAW) ya ce: “Wane ne mafi hakkin mutane ga in kyautata zamana da shi?” Sai ya ce: “Mahaifiyarki.” Ya ce, “Sai kuma wa?” Ya ce: “Sa’annan mahaifiyarka.” Sa’annan ya ce: “Sai kuma wa?” Ya ce, “Mahaifiyarka.” Ya ce, “Sai kuma wa?” Ya ce, “Sa’annan mahaifinka.” (Buhari Hadisi na 5971 da Muslim Hadisi na 2548).
Anas bin Malik ya ce: “Na ji Manzon Allah (SAW) yana cewa: “Wanda yake son a yalwata masa arzikinsa ko bayansa ya yi albarka, to ya sadar da zumuntarsa.” (Buhari Hadisi na 5985 da Muslim Hadisi na 2557).
Adda’u ya ce: “Dirhamin da na bayar da shi ga dangina ya fi min dadi daga Dirhami dubu da na ciyar da waninsu. Sai wani ya ce masa: “Ya Abu Muhammad koda dangina sun kai ni wadata?” Ya ce: “Koda sun fi ka wadata.” (Mukarimul Akhalak na Ibnu Abu ad-Duniya, shafi na 62).