Babu abin da kowane Musulmi ya fi son samu a watan Ramadan kamar samun gafara da rahamar Allah da kuma dacewa da shiga Aljanna.
Ga wasu hanyoyi da ayyukan lada bakwai da mutum, musamman mai azumi, zai aikata domin yi wa kansa guzuri da samun dacewa da irin alheran da Allah Ya tanada a Aljanna kamar haka:
1- Samun masauki a Aljanna
Tabbas, tun daga duniya mutum zai iya sama wa kansa masauki na musamman a Aljanna. Amma ta yaya?
A wani Hadisi na Abu Huraira (RA), Manzon Allah (SAW) ya ce, “Duk wanda ya je dubiyar mara lafiya, wani mai kira zai rika kiran shi daga sama yana cewa ka ji dadi, tafiyarka ta yi kyau, kuma ka samu masauki a cikin Aljanna.”
Haka kuma, Manzon Allah (SAW) ya ce, “Idan Musulmi ya je ya gaishe da dan uwansa (mara lafiya) zai kasance ne a kan hanyar Aljanna, har sai ya dawo.”
Lallai zuwa duba marasa lafiya abu ne da bai kamata a yi wasa da shi ba, musamman ga mai azumi.
Uwa uba, gaishe da mara lafiya yana daga cikin hakkin Musulumi a kan dan uwansa Musulmi.
2- Kalmar da za ta shigar da kai Aljanna
Manzon Allah (SAW) ya ce, duk wanda ya ce La ilaha illal Lah, da tsarkin zuciya, to zai shiga Aljanna.
A wani Hadisi, Annabi Musa ya roki Allah Ya ba shi wani zikiri da ba a taba wa ba wa wani kamarsa ba, sai Allah Ya ce mishi Ya Musa, ka ce La ilaha illal Lah.
Annabi Musa ya ce, Ya Allah ai bayinKa suna cewa La ilaha illal Lah.
Allah Ya ce mishi, Ya Musa, da za a dauki duniya da abin da ke cikinta a sanya hannu daya na sikeli, sannan a dauki La ilaha illal Lah a sanya a daya hannun sikelin, da sai La ilaha illal Lah ta rinjaye wancan.
Saboda haka yana da kyau a yawaita wannan zikiri mai girma, musamman a wannan wata mai alfarma na Ramadan.
A wani Hadisi, Annabi (SAW) ya ce mafi alherin ambaton Allah da shi da sauran annabawa da suka gabace su suka fada shi ne La ilaha illal Lah, wahdahu la sharika lah, lahul mulku wa lahul hamd, wa huwa ala kulli shai’in kadir.
3- Samun hasken kabari
Kamar yadda muke rokon Allah Ya haskaka mana kabarinmu, haka muke kyautata zaton cewa duk wanda ya samu hasken kabari to zai dace a Lahira.
Cikin rahamar Allah ga bayinSa, Ya samar mana da wata hanya da tun daga duniya za mu iya yi wa kanmu tanadin hasken kabari idan muna kula da kuma haskaka dakunanSa, wato masallatai.
Umar bin Khattab ya ruwaito daga Manzon Allah (SAW) cewa, “Duk wanda ya sanya haske a wani masallaci to Allah zai haskaka kabarinsa.
“Sannan duk kuma wanda ya sanya kamshi (turare) mai dadi a masallaci, to Allah zai sanya kamshin Aljanna a kabarinsa”.
Za ka iya samun wadannan garabasa gwargwadon karfin aljihunka, ta hanyar taimaka wa masallaci da kudin wuta, sayen janareta ko man janareta, gyaran wuta ko biyan kudin aikin, sayen kwan lantarki, sadakar turaren wuta da sauransu.
4- Saura kiris ka shiga Aljanna
Ayatul Kursiyyu ita ce aya mafi girma a cikin littafin Allah, Al-kur’ani.
Manzon Allah (SAW) ya bayyana cewa duk wanda ya karanta Ayatul Kursiyyu bayan sallar farilla, to babu abin ya rage mishi ya shiga aljanna a wannan lokaci face ya mutu.
5- Afuwar Allah a Ranar Hisabi
Duk mutumin da za a yi mishi binciken kwakwaf, to ya shiga uku, ba zai kai labari ba. Ina ga mutumin da mala’iku ne za su bincike shi bisa umarnin Allah (SWT)!
Amma Allah Majikan Bayi ya sama wa bayinSa wani aikin alheri wanda idan muna aikatawa to za mu samu rangwame daga gareShi a Ranar Sakamako.
Wannan abu kuwa shi ne tausaya wa wanda muke bi bashi — idan muka jinkirta wa wanda muke bi bashi a duniya, Allah zai rangwanta mana a Ranar Hisabi.
Huzaifa ya ruwaito cewa Manzon Allah (SAW) ya ce, “Bayan mala’iku sun dauki ran wani mutum daga cikin al’ummomin da suka gabace ku, sai suka tambaye shi, shin akwai wani aikin alheri da ka taba yi a duniya? Mutumin ya ce babu.
“Sai suka ce mishi ka yi tunani dai. Sai ya ce, ‘Na kasance a duniya ina ba wa mutane bashi, kuma ina umartar yarana (da ke zuwa karbo bashin) cewa su jinkirta wa duk mutumin da ba shi da shi (har sai ya samu abin da zai biya)….” Sai Allah Ya ce wa malai’ku, “Ku yi mishi afuwa.”
6- ’Ya’yan itatuwan Aljanna
’Ya’yan itatuwan aljanna sun wuce duk yadda mutum yake tunani wajen yawan nau’ikansu da nunarsu da dadin dandanonsu da kuma gamsarwa.
Yadda mutum, musamman mai azumi, zai bi domin samun wannan kayan marmari na gidan Aljanna shi ne ta hanyar ciyar da mayunwaci.
Hadisin Abu Sa’idil Khudri ya ruwaito daga Manzon Allah (SAW) cewa, “Duk muminin da ya ciyar da wani mumini da ke jin yunwa, to a ranar Alkiyama Allah zai ciyar da shi daga ’ya’yan itatuwan Aljanna.
“Duk muminin da ya shayar da wani mumini mai jin kishi, to Allah zai shayar da shi daga Al-Rahikul Makhtum (ruwan furen Aljanna).
7- Samun taskar Aljannah
Taska abu ne mai matukar daraja wadda ba a iya yi mata kima da kudi a wani lokaci. Ina ga a ce taskar a cikin Aljanna take!
Amma daga nan duniya mutum zai iya yi wa kansa tanadin taska a cikin Aljanna kuma ya samu hakan, ta hanyar ambaton La haula wa la kuwwata illa billah.
Manzon Allah (SAW) ya ce La haula wa la kuwwata illa billah taska ce daga cikin taskokin Aljanna.
Allah Ya sa mu dace. Amin.