Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar ya yi wa Gwamantin Najeriya shagube game da karin farashin man fetur wanda gwamantin ta ce ya faru ne saboda janye tallafi.
- Atiku ya wallafa a shafinsa na Twitter da safiyar Talata, yadda yake mamakin karuwar kudin man a Najeriya alhali farashin danyen mai a kasuwannin duniya na ta raguwa tun daga 2019.
- Abin da ya sa muka yi karin farashin mai
- Sarakunan Arewa na taro kan tsaro a kan matsalar tsaro
- An hako akwatunan gawa da masu shekara 2,500 a Masar
“Ni dan kasuwa ne kuma ina kallon abubuwa ne ta fuskar tattalin arziki. Ina da tambayoyi masu bukatar amsoshi.
“Farashin danyen mai ya ragu daga yadda yake a 2019 kuma a Amurka da Turai farashin mai ya ragu sosai daga yadda yake a 2019.
“Idan da gaske gwamanti ta cire hannunta, shin ba kamata ya yi a ce farashinsa ya ragu ba?
Bayannin na Atiku na zuwa ne washegarin ranar da Shugaban Kasa ya yi bayani ta bakin Mataimakinsa, Yemi Osinbajo, game da abin da ya haddasa karin farsashin.
Buhari ya ta’allaka karin rashin da illar da annobar COVID-19 ta yi wa tattalin arziki a fadin duniya da kuma faduwar kudin danyen mai.
Hakan ta sa gwamanti ta cire hannunta daga kayyade farashin mai, ta bari yanayin kasuwar danyen mai ya yi alkalanci.
Ya ce yanayin da aka tsinci kai a ciki ya tilasta wa gwamnati yin sauye-sauye da za a ci moriyarsu a nan gaba duk da cewa da farko ba za a ji dadinsu ba.
Ya ce matakan sun hada da daina bayar da tallafin mai saboda yawan kudaden da ake kashewa a kai.
Maimakon haka za a sanya kudaden wajen a bangarorin ilimi da laifiya da sauran muhimman abubuwa na rayuwar ‘yan kasa.