Tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya kuma dan takarar shugaban kasar Najeriya a jam’iyyar PDP Atiku Abubakar, ya yi alkawarin inganta noma da harkokin kasuwanci idan aka zabe a matsayin shugaban kasar Najejriya.
Dan takarar ya bayyana hakan ne yayin kaddamar da yakin neman zabensa a filin wasa na Sani Abacha jihar Kano. Atiku ya bayyana irin rashin jin dadinsa game da durkushewar masana’antu a duk fadin Najeriya kuma ya dauki alwashin farfado da su idan har ya lashe zaben shugaban kasar Najeriya.