Dan takarar Shugaban Kasa na Jam’iyyar PDP Alhaji Atiku Abubakar, ya tafi Amurka domin ci gaba da yakin neman zabensa ga ’yan Najeriyar mazauna Amurkan.
Cikin wata sanarwa da kungiyar yakin neman zabensa ta fitar, ta ce Atikun zai shafe mako guda ne a Amurkan, domin ganawa da ’yan Najeriya daban-daban.
- Mutum 14 sun rasu, gidaje 50 sun salwanta a ambaliyar Gombe
- Kotu ta yanke mata daurin rai-da-rai kan mutuwar mijinta
“A kokarinsa na tafiya tare da kowa yayin da yake Amurka, Atiku zai gana da ’yan Najeriya mazauna kasashen waje, da kuma ’ya’yan jam’iyyar PDP da ke Arewacin Amurka.
“Zai kuma gana da jagororin ’yan kasuwar Najeriya, daga nan kuma ya gana da matasa”, a cewar sanarwar.
Makonni uku da suka gabata ne dai Atiku ya fara yakin neman zabensa a Akwa Ibom, babban birnin Jihar Uyo da ke Kudancin Najeriya.
Daga nan ne kuma ya zarce Jihar Kaduna da ke Arewacin Najeriya, da Benin, babban birnin Jihar Edo da ke Kudu.
A ranar Litinin ne kuma a ke sa ran zai dawo Najeeriya, washegari Talata kuma ya wuce Jihar Ekiti, sai Laraba ya wuce Ondo duk domin yakin neman zaben.