Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya yi kira da kakkausar murya ga Kungiyar Malaman Jami’o’i ta Kasa (ASUU) da ta dakatar da yajin aikin da take yi tsawon lokaci.
Shugaban ya yi wannan kiran ne yayin da yake karbar wasu Gwamnonin jami’iyyar APC da suka kai masa ziyarar Sallah mahaifarsa ta Daura da ke jihar Katsina a ranar Litinin.
- 2023: Me ya sa sanatocin APC ke ficewa zuwa wasu jam’iyyun?
- An gano gawar mutum 15 da suka mutu a hatsarin jirgin ruwan Legas
Buhari ya tabbatar wa Gwamnonin cewa Gwamnatinsa na sane da matsayarta kan batun, kuma tattaunawa za ta ci gaba amma sai dalibai sun koma makarantu.
Cikin wata sanarwa da Kakakin Shugaban, Garba Shehu ya fitar, Buhari ya ce suna cikin damuwa kan yadda hakan zai shafi ba ma iya daliban kadai ba har da iyalansu, da tsarin Ilimin kasar nan, da ci gabanta na tsawon lokaci.
Haka kuma ya ce yajin aikin tuni ya fara shafar tunanin iyaye da dalibai da sauran masu ruwa da tsaki, inda suka watsar da lamuran tarbiya da ke karkashin kulawarsu.
Kazalika, ya ce ci gaban Najeriya kacokan ya ta’allaka ne kan ingantaccen ilimi da makarantun da za su bada su.
Ya ce, “Muna fatan ASUU za ta jikan al’ummar kasa ta janye yajin aikin da ta ke yi. Tura ta kai bango kan ajiye dalibai a gida. Saboda Allah ina dalilin cutar da ‘ya’yan mu da za su zo a gaba da ba su ji ba ba su gani ba?”
Kazalika Buharin ya yi kira ga masu fatan Najeriya ta ci gaba, musamman wadanda suke da kusanci Shugabannin kungiyoyin jami’o’in da su jawo hankalinsu kan illolin da yajin aikin ke haifarwa kasa da kuma wadanda za su haifar a nan gaba.
Buhari ya kuma ce dalibai daga jami’o’in Najeriya za su fuskanci kalubalen gasa da takwarorinsu da ke sauran jami’o’n duniya, musamman a bangaen fasahar kere-kere, domin acewarsa ajiye su a gida yana hana su samun lokaci, da ilimi, da ma damar da zai sa su yi kafada da kafada da sauran daliban duniya.
“Ilimin da turawan mulkin mallaka suka zo mana da shi, an tsara shi ne don samar da ma’aikatan gwamnati. Yanzu kuwa sanin kowa ne babu aikin. Ya kamata yanzu matasanmu su samu ilimi don su dogaro da kansu.
Buhari ya ce kamata ya yi a kara amfani da albarkatun kasa wajen gina ababen more rayuwa da gudanar da harkokin kiwon lafiya da ilimi, ba wai a fadada tsarin mulki don samar da ayyukan yi ga matasan ba.
A na sa bangaren shugaban kungiyar gwamnonin APCn Abubakar Atiku Bagudu, ya godewa shugaban bisa rawar da yake takawa wajen inganta tattalin arzikin kasa da dimbin nasarorin da aka samu a jam’iyyar ta su, wadanda suka hada da tarurruka biyu da aka gudanar har suka samar da shugabancin jam’iyyar., da kuma dan takarar shugaban kasa, Asiwaju Bola Tinubu.