Kungiyar Malaman Jami’o’i ta Kasa (ASUU) ta sha alwashin maka Hukumar Tsaron Farin Kaya ta DSS a kotu bisa zargin cin zarafin jami’inta na shiyyar Kano, Farfesa Abdulkadir Mohammed.
Shugaban kungiyar reshen Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya, Farfesa Rabiu Nasiru ne ya sanar da haka a ganawar sa da manema labarai a Zariya ranar Juma’a.
- ’Yan bindiga sun kai hari kauyen Abuja, sun yi awon gaba da mutum 2
- Mahaukaciyar Guguwar ‘Ida’ a hallaka mutum 36 a Amurka
Nasiru ya ce al’amarin ya auku ne a ranar 18 ga watan Augustan 2021 wanda ya ce harkan ya saba wa yancin dan Adam.
A cewarsa, abin takaici ne a ce hukamar da aka samar da ita tun zamanin turawan mulkin mallaka a shekarar 1948, domin ba da tsaron cikin gida amma sai ta rikide da koma tana cin zarafin al’umma.
Farfesa Rabiu ya ce wannan ba shi ne karon farko da hukumar ke cin zarafin masu mutunci ba domin a baya ma ta kama tare da tozartar da editan mujallar Newswatch a shekarar 1988, da kuma editan jaridan mujallar Tell.
Ya kuma yi zargin cewa hukumar ta kasance ta ke gudanar da aikinta na cin zarafin ’yan kasa a maimakon kare mutuncin su.
Shugaban na ASUU ya ce a kan haka suke kira ga hukumar ’yan sanda ta kasa da lallai ne ta gano wadanda suka aikata haka tare da ladaftar da su tare da tabbatar da an gyara motarsu da aka fasa, in bah aka ba kuma su garzaya kotu.
Ya kuma yi kira ga ’yan majalisa na kasa da su sake duba kundin dokar da ya samar da hukumar domin yi mata kwaskwarima.