Kungiyar Malaman Jami’o’i ta Najeriya (ASUU) ta sanar da mayar da yajin aikin da take yi zuwa na har sai abin da hali ya yi.
Daukar matakin ya biyo bayan taron Kwamitin Zartarwar Kungiyar na kasa da aka yi a daren Lahadi, duk da yake kungiyar ba ta yi cikakken bayani a kan sake tsawaita yajin aikin ba.
Tun a ranar 14 ga watan Fabrairu ne dai kungiyar ta sanar da tsunduma yajin aikin bayan ta zargi Gwamnatin Tarayya da kin mutunta yarjejeniyarsu tun ta shekarar 2009.
Hakan na zuwa ne duka da Gwamnatin Tarayya na ikirarin cewa tana dab da cim ma matsaya don kawo karshen yajin aikin.
A baya dai, Minista a Ma’aikatar Kwadago, Festus Keyamo, ya ce Gwamnatin Tarayya ba za ta dakatar da ayyukanta ba domin sauraron bukatun kungiyar.
Ministan dai ya ce Gwamnati ta yi iya bakin kokarinta, inda ya bukaci iyayen daliban da su nemi malaman su koma makaranta.
Tun fara yajin aikin dai, akalla kungiyoyi daban-daban ne suka yi yunkurin shiga tsakani, amma har yanzu kwalliya ba ta biya kudin sabulu ba.
Daga cikin bukatun akwai maye gurgin tsarin biyan albashi na IPPIS da UTAS, biyan bashin kudaden alawus-alawus ga malaman jami’a da kudadeninganta jami’o’i da sauransu, da dai sauransu.