Kungiyar Malaman Jami’oi ta Kada (ASUU) ta zargi Gwamnatin Tarayya da kin aiwatar da yarjejeniyar da suka cimma a watan Disambar bara.
Kungiyar dai ta yi barazanar sake tsunduma yajin aiki saboda ta ce shi ne matakin karshe da za ta iya dauka kuma shi ne kadai ne yaren da gwamnatin take fahimta.
- Kabiru Gombe zai maka tsohon kwamishinan Kano a kotu
- An fara mayar da ’yan gudun hijirar Zamfara garuruwansu
Jami’in kungiyar na shiyyar Kano, Farfesa Abdulkadir Muhammad ne ya sanar da hakan yayin da yake jawabi ga wani taron manema labarai a Kano ranar Juma’a.
Ya ce kungiyar za ta bi dukkan matakan da suke cikin doka wajen ganin ta kai ga gaci, ciki har da tattaunawa da jama’a da kuma gwamnati.
Farfesa Abdulkadir ya ce shiyyar ta su wacce ta kunshi jami’o’i bakwai a karshen taronta na ranar Juma’a ta duba batun aiwatar da tanade-tanaden yarjejeniyar ta watan Disambar bara wanda ya mayar da hankali akan kudaden da suke bi na alawus-alawus.
Ya ce yarjejeniyar dai ta tanadi lokacin aiwatar da dukkan batutuwan da aka amince a kansu, amma gwamnati ta ki cika alkawuranta.
“Kada ’yan Najeriya su zargi kowa sai gwamnati muddin aka sake samun tsaiko a kalandar karatun jami’o’i.
“Kungiyarmu a shirye take ta dauki kowanne irin mataki da zai ceto jami’o’in Najeriya daga durkushewa,” inji shi.