✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Asusun ITF ya koya wa matasa dubu 37 sana’o’i a Najeriya

Asusun haror da ma’aikata na kasa [ITF] da ke garin Jos, babban birnin Jihar Filato ya koya wa matasan Nijeriya sama da dubu 37 sana’o’i…

Asusun haror da ma’aikata na kasa [ITF] da ke garin Jos, babban birnin Jihar Filato ya koya wa matasan Nijeriya sama da dubu 37 sana’o’i daban-daban a shekarar da ta gabata.
Darakta Janar na asusun, Farfesa Longmas Wapmuk ne ya bayyana haka a lokacin da yake jawabi a wajen bikin karrama ma’aikatan na ITF da suka yi fice na wannan shekara ta 2014 da aka gudanar a Jos.
Ya ce babu shakka asusun na ITF ya gudanar da ayyukansa na horar da matasan kasar nan sana’o’i daban-daban kamar yadda ya kamata, a shekarar 2013.
Farfesa Longmas ya yi bayanin cewa wadannan matasa da suka horar, sun fito ne daga hukumomi da  kungiyoyi masu zaman kansu na jihohin Najeriya, kuma yanzu haka wasu sun sami ayyukan yi a hukumomi da kamfanoni masu zaman kansu, a yayin da wasu kuma suka sami sana’o’in dogaro da kansu.
Ya nuna takaicinsa kan yadda asusun ya kasa gudanar da ayyukansa na horar da matasa a jihohin Barno da Yobe saboda matsalar tsaro da ake fama da ita a jihohin.
Ya ce a halin yanzu akwai miliyoyin daliban Najeriya da asusun yake horarwa. Don haka ya yi kira ga gwamnatin Najeriya kan ta tallafa wa asusun da kudade domin ya ji dadin gudanar da ayyukansa.
A nasa jawabin, Gwamna Jonah Jang na Jihar Filato ya yaba wa asusun ne kan kokarin da yake yi wajen koya wa matasan Najeriya sana’o’in hannu da za su iya dogara da kansu.
Gwamnan, wanda kwamishinar ciniki da masana’antu, Misis Helen Maina ta wakilta, ya ce babu shakka Jihar Filato tana alfahari da kasancewar asusun na ITF a jihar ta Filato, domin tattalin arzikin jihar yana bunkasa sakamakon kasancewar asusun a jihar.