✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Asarar-dan-kwabo

Asarar-dan-kwabo, wani babban mugun daji ne dan Hauren-Danja, wanda ya taba zama ja-gaban kungiyar bunburutu buruntun satar mai , wadda ta fake da fafutikar ’yanci,…

Asarar-dan-kwabo, wani babban mugun daji ne dan Hauren-Danja, wanda ya taba zama ja-gaban kungiyar bunburutu buruntun satar mai , wadda ta fake da fafutikar ’yanci, ta kuma jefa al’umma cikin kangi. A da Asararren dokin-bobo ya tuba daga tayar da kan adda, amma da aka wayi gari ya fasko cewa ragamar Haurobiya na hannun dan yankinsu, sai tsiya da wasali kasa yake ta cakowa, wato dai tsi ta ja ya, ita ce tsirin tsiren tsiyataku!
Asarar-dan-kwabo da wani dan yankinsu mai suna Kansakalin Kuku sun taba yin ikrarin cewa matukar aka daina Gudun-loko da Jona-tantin mulki a Haurobiya, to sun daura yaki da kasar nan ke nan. Ganin abin da ya auku ga Ja-gaban masu fafutikar Burin-huriyya, inda aka jefa masa gurneti da nakiya, a daidai lokacin da ya bar Jihar Bayan-Kada da zummar zuwa birnin Daurama da ke Jihar dakin-kara. Sannan a dai wannan ranar Ta-bawa ranar samu (inji mai bara) aka auka wa Addahiri Shehi na Baubawan-cici, shi ma dai Mai-duka ya ba shi kariyarSa, domin gurneti da nakiya ba su yi tasiri a kansa ba, duk da cewa an yi asarar rayukan al’umma.
Masu koyon watsattsake da buda wagagen littattafai a wannan farfajiya ta Dodorido da ke cikin Amintatar jaridar Haurobiya, abin da ya kamata mu fasko a irin wannan yanayi shi ne, Asarar-dan-kwabo da Kansakalin-kuku da tsoho Kilaki da jiga-jigan jam’iyya mai dan boto da sanda jirge sun kaddamar da yaki a kan Arewacin Haurobiya. Domin mugun daji ya bayyana a jaridu da mujallu da akwatunan batu masu kwakwazo da masu baje dodon hotuna, cewa Arewatawa magabtan Jatau ne, don sun nuna kiyayyarsu ga Gudun-loko da Jona-tantin mulki. Asarar-dan-kwabo, ya mayar da kansa tundurkin bangar Shugaban kasar Haurobiya. Don haka a shirye yake ga duk wanda ya ce wa ubangidansa kulle, shi kuwa zai ce masa “cas! Cas!! Cas!!”
A irin kwakwariyar tundurki Majahadin fada, ya bayyana cewa Ja-gaban Haurobiyawa mai fafutikar Burin-huriyya, shi ya shirya kaddamar wa kansa harin gurneti da nakiya. Kai wannan hankalinsa a hannun riga yake, domin mai hankali a kwakwalwarsa ba zai taba yarda da irin wannan shaci fadin ba; kuma in ban da tabin kwanya yaya za a yi mutum ya sanya akai masa mummunan hari?
Haurobiyawa ku shiga taitayinku, al’amuran da ake tsuwurwurtawa a kasar Haurobiya na nuni da cewa babu wanda ke da sulke da garkuwa. Kuma jami’an tsaron Haurobiya sun zama ’yan wasan Samson-siya-siya, inda ake damawa da su a dama-dama-da-kurda-kurdar siyasar jam’iyya mai dan boto da sanda jirge. Wannan dalilin ne ya sanya kuka ga ana ta yi wa al’umma Damo-da-kura-da-diyya.
Babban lamarin da ke jan hankalin al’umma, yana dada jefa musu alamomin tambaya a kwakwalensu, shin wace manufa ake son cimmawa; ko dai wasattsaken wasikar Baba-ojo mai gonakin Ottawa ta tabbata; uwa-uba ko Shagaban kasar Haurobiya ya doge kan lallai ko ana ha maza, ha mata sai ya ci gaba da jan ragamar Haurobiya a shekara ta dubu karamin lauje da sili da baban lauje?
Batu na ingarman karfen karafa, manya da kananan Haurobiyawa sun san amsar tambayoyin da na bijiro da su. Sannan an tabbatar jihohin Bararon-nono da Yawon-Bebe kai da daukacin Arewacin Haurobiya idan har aka kyale talakawa suka kada kuri’unsu, don zaben jagora nagari, gwamnati mai ci yanzu da mukarrabanta ba za su taba kai bantensu ba. Don haka aka fake da yamutsin Haramta Bobo da kwambon bokoko ana nakasa al’umma a daukacin fadin Arewa.
Hasali ma dai so ake yi ku daina koyon watsattsake da buda wagagen littattafai, a kowane fanni na bokoko ko saukakken littafi daga Mai-duka, ballatana kalaman fiyayyen halitta. Ni kuwa na sha ji manyan masanan zaure na furta cewa, “la fakaru ba’adil ilimi – wato babu talalar talauci bayan ilimi.” Kuma mashahurin Babban mutum mai maka-wuya na kasar Sawun-diyyar Larabawa, ya taba furtawa, cewa, “man lam yakra’u tarikh lam ya ish – wato duk wanda bai akranci tarihi ba, ahkika ba zai rayu ba.” Don haka mu yunkura wajen fafutikar yaki da juhala don tabbatar da adala.” Asarar rayukan da ake yi babbar musifa ce, fiye da asarar kwabban da ba za su tsinana wa kowa komai ba. Mu daina tafka alfasha da munkari da sauran miyagun ayyuka.
Lallai kowa ya baje na-mujiya, a zuba na-zomo; mu yi kokarin rage kwalama, ko da masu wasan Samson-siya-siya da dama-dama-da-kurda-kurdar siyasa sun raba kayan makwalashe kada mu karba, domin kowa ya ci ladar na-dajine, dole ne ya yi masa kwal a kwabo. Shin ba ku gani, tun sa’adda Asararren Dokin-bobo ya fara kwasar lagwada a fadar mulkin Haurobiya, har ya sauya sunansa zuwa Asarar-dan-kwabo, wato idan mulki ya subuce musu, yana ganin zai asarar kwabban da yake cika lalitarsa da su.  Sai a kara himma wajen neman agajin Mai-duka, domin kada mu tashi babu lada, ba la’ada.
Mu yi duk abin da za mu iya yi wajen tabbatar da cewa Gwmanatin Haurobiya ta taka wa Asarar-dan-kwabo burki, idan kuwa ta kiya, ai mu ma sai mu kaddamar kin biyayya gareta, ta yadda za ta rasa wadanda za ta mulki. Kodayake ban abin da ya faranta raina, shi ne, wani aminina da ke aiki a Babban Bakin Ce ce ku ce na Birnin Lantsandan, ya tabbatar mini da cewa, a halin yanzu ’yan Hauren-Danja da kansu ke mayar da martini ga Asarar-dan-kwabo. Duk mai son ya tabbatar da wannan batu, sai ya baje na-zomonsa wajen nazarin shafukan mashakatar lilo da tsallake-tsallake, wadanda suka ahda da Fuskantar-boko da na Tuwon-titi!