✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Arsene Wenger ya bayyana dalilin yin watsi da kungiyar Manchester

Mai horar da ’yan wasan Kungiyar kwallon kafa ta Arsenal, Arsene Wenger ya ce kimar da ke cikin kungiyar kwallon kafa ta Arsenal ne ta…

Mai horar da ’yan wasan Kungiyar kwallon kafa ta Arsenal, Arsene Wenger ya ce kimar da ke cikin kungiyar kwallon kafa ta Arsenal ne ta sanya ya ki amincewa da bukatar kungiyar kwallon kafa ta Manchester na neman ya maye gurbin mai horar da ’yan wasan kungiyar, Alex Faguson.
Tsohon Shugaban kungiyar kwallon kafa ta Manchester, Martin Edwards ne ya bayyana haka a littafin tarihinsa cewa shi da tsohon shugaban kungiyar, Peter Kenyon sun tuntubi Wenger har sau biyu don su tattauna maye gurbin Ferguson bayan da ya bayyana cewa zai yi ritaya a shekarar 2002.  
Lokacin Wenger yana dab da jagorantar kungiyar Arsenal zuwa cin kofin Firimiya da kuma  gasar kofin kalubalen cikin shekaru biyar.